‘Yan Adawa Sun Fara Yabawa a Kano, Abba Ya Yi Bayanin Yadda Yake Inganta Lantarki

‘Yan Adawa Sun Fara Yabawa a Kano, Abba Ya Yi Bayanin Yadda Yake Inganta Lantarki

  • Abba Kabir Yusuf ya yi bayanin yunkurin da suke yi na ganin Kanawa sun samu isasshen hasken wutar lantarki
  • Gwamnan jihar Kano ya tabbatar da karasa aikin lantarkin da Rabiu Kwankwaso ya fara a lokacin ya na mulki
  • Abba ya kuma ce ya roki gwamnatin tarayya ta yi kokarin ganin an taimakawa jihar Kano a bangaren wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ganin yadda ake fama da matsalar wutar lantarki a Najeriya, Kanawa sun fara neman jin kokarin da gwamnansu yake yi.

Abba Kabir Yusuf ya shaidawa duniya yadda zai inganta harkar wutar lantarki a Kano domin bunkasa kasuwanci da jin dadin al’umma.

Abba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya na kokarin inganta lantarki Hoto: Abba Kabir Yusuf/@NazeerTukuntawa
Asali: Facebook

Wutar lantarki: Wani hali ake ciki a Kano?

Mai girma gwamnan Kano ya yi wannan bayani ne a shafin X a ranar Juma’a, 8 ga watan Nuwamba 2024 bayan tambaya da aka yi masa.

Kara karanta wannan

TCN: Ƴan Najeriya za su ɗauki lokaci ba wutar lantarki, an gano matsaloli 3 a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hajiya Maryam Waleeda ta nemi jin ta bakin Abba Kabir Yusuf game da batun lantarki ganin cewa akwai madatsun ruwa a jihar Kano.

Abba ya dage kan matsalar wutar lantarki

Gwamnan ya ba da amsa da cewa tare da yi mata gyara cewa jihar Kano ta na da madatsu har 20 kuma kowane yana da aikin da yake yi.

Abba ya ce gwamnatin Kwankwaso ta dauko aikin samar da lantarki daga Tiga kuma a yanzu sun kammala, an samu megawatts 10.

Da wannan madatsa ake samun wuta a rukunin gidajen Kwankwasiyya da wasu kamfanoni, kuma ana kan aikin Challawa-Gorge.

Idan an karasa aikin madatsar Challawa-Gorge da yanzu ya yi nisa, gwamna Abba ya ce za a samu megawatt shida na karfin lantarki.

Ana so gwamnatin tarayya ta taimakawa Kano

Yayin da ministan makamashi ya ziyarci Kano kwanan nan, Alhaji Abba ya bayyana cewa ya roke shi a kara wutar da ake ba jihar.

Kara karanta wannan

Lauyan yara da su ka yi zanga zanga ya fadi yadda gwamna Abba ya agaza masu

"Sannan na kuma roki gwamnatin tarayya game da bangare na biyu na aikin tashar Kaduna-Kano 330KC da Daura-Jogana-Kura 330KC...
"tare da fara aikin samar da lantarki daga hasken rana a jihohin Arewa 19 da aka amince da shi."

- Abba Kabir Yusuf

Abba ya samu yabon 'yan adawar Kano

Da jin wannan aka ji hatta ‘yan jam’iyyar APC a shafin X irinsu Bashir Ahmad suna yabawa yunkurin gwamna Abba da ya shiga ofis a 2023.

Shi ma a shafinsa na Facebook, tsohon kwamishina a mulkin APC, Injiniya Muaz Magaji ya nuna ya fara gamsuwa da gwamnatin NNPP.

“Sakamakon tambayoyi da shawarwarin da kanawa ke ta mika wa Abba! Gwabna yayi bayani kan tsarin Samar da wutar lantarki a Kano da na yarda da shi kuma na yaba masa, lallai na fara Amincewa da tukin Abba!”

- Muaz Magaji

Kira ga gwamna Abba Yusuf kan zaben Kano

Kara karanta wannan

An fara dawo da wutar lantarki a yankuna, TCN ya bukaci a kwantar da hankali

Ana da labari cewa Barista Ibrahim Arif Garba ya ba gwamnan Kano ya sallami shugabannin KANSIEC saboda gudun a samu matsala.

A maimakon gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura sunan sababbin shugabannin hukumar zabe majalisa, sai ya bi wata hanya dabam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng