Bayan Sauke Masu Mukamai a Gwamnati, Gwamna Ya Fallasa Shirin APC
- Gwamnan jihar Edo mai barin gado, Godwin Obaseki ya nuna yatsa ga jam'iyyar APC mai shirin karɓar ragamar mulki a hannunsa
- Godwin Obaseki ya yi zargin cewa jam'iyyar APC ta ciyo bashin N2bn zuwa N5bn domin bikin rantar da Sanata Monday Okphebolo
- Obaseki ya bayyana cewa ba a yi shawara da gwamnatinsa ba sannan kuma ko gayyatarsa ba a yi ba zuwa wajen bikin rantsarwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo mai barin gado, Godwin Obaseki ya yi zargin cewa jam’iyyar APC ta ciyo bashin Naira biliyan biyu zuwa Naira biliyan biyar.
Gwamna Obaseki ya yi zargin cewa APC ta ciyo bashin ne domin gudanar da bikin rantsar da zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Sanata Monday Okpebholo, wanda aka shirya yi ranar 12 ga watan Nuwamba.
Gwamna Obaseki ya bayyana hakan ne a Benin a yayin rantsar da kwamitin riƙo na jam’iyyar PDP reshen jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane zargi Gwamna Obaseki ya yi wa APC?
Ya koka da cewa a matsayinsa na gwamna mai barin gado, jam’iyyar APC ba ta shawarci gwamnatinsa ba sannan kuma ba ta gayyace shi zuwa bikin rantsarwar ba.
"Muna da kusan Naira Biliyan 27 da za mu biya kuɗaɗen ayyuka, amma sun fara ɓarnatar da su, kuma sun je sun karɓo bashin Naira biliyan biyu zuwa biyar domin bikin rantsarwa. Kudin da za su fara cira kenan daga asusun ajiya."
"Suna yin bikin rantsarwa amma ba a gayyaci gwamna ba. Kamar sun fara sabuwar gwamnati da sabuwar jiha."
- Gwamna Godwin Obaseki
Gwamna Obaseki ya kuma tabbatarwa da ƴaƴan PDP cewa ba zai yi nisa da jam’iyyar ba domin zai ci gaba da zama domin bayar da shawarwari.
EFCC na shirin cafke Obaseki
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya ce ya samu labarin hukumar yaƙi da rashawa watau EFCC na shirin cafke shi bayan ya miƙa mulki a makon gobe.
Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana hakan ne a taron EdoBEST na kasa wanda ya gudana a Abuja ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng