'Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa da Mutane, Sun Kwato Makamai
- Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun samu nasarar cafke wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar masu garkuwa da mutane ne
- Ƴan sandan sun cafke waɗanda ake zargin ne su uku bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu na addabar mutane a titin hanyar Kaduna-Abuja
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da cafke nutanen ya ce an ƙwato makamai a hannunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane.
Tawagar ƴan sanda na Operation Fushin Kada sun cafke mambobi uku na wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane waɗanda suka addabi matafiya a hanyar Kaduna-Abuja da jihohi makwabta.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan ya fitar a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa waɗanda aka zargin masu suna, Muhammad Lawal Abubakar, Abubakar Isah Samaila Saidu an cafke su bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu.
Ya bayyana cewa an ƙwato bindiga ƙirar AK-47 tare da jigida wacce babu komai a cikinta a hannun waɗanɗa ake zargin.
Ya bayyana cewa a lokacin da ake yi wa waɗanda ake zargin tambayoyi, sun amsa cewa suna cikin ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ta addabi titin hanyar Kaduna-Abuja, rahoton The Nation ya tabbatar.
ASP Mansur Hassan ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin na ba ƴan sanda haɗin kai wajen ba da bayanan da za su taimaka a cafko sauran mambobin ƙungiyar da ƙwato makaman da ke hannunsu.
Rikicin soja da ƴan sanda ya jawo asarar rai
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayukan mutum biyu biyo bayan ɓarkewar rikici tsakanin wani soja da wani jami'in ƴan sanda na musamman a jihar Nasarawa.
Rahotanni sun nuna cewa an samu rikicin ne a ranar Lahadi a kasuwar Agyaragu da ke ƙaramar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.
Asali: Legit.ng