An Shiga Tashin Hankali a Filato, Ana Zargin Jami'an NDLEA Sun Kashe Wani Matashi

An Shiga Tashin Hankali a Filato, Ana Zargin Jami'an NDLEA Sun Kashe Wani Matashi

  • An zargi jami'an hukumar NDLEA da kashe wani matashi, Faisal Yakubu Hussaini yayin farmaki a garin Dangi a jihar Filato
  • Al'ummar yankin Kanam sun yi Allah wadai da wannan aika aikar, inda suka nemi NDLEA ta dauki mataki kan jami'an nata
  • Hukumar NDLEA ta yi martani kan wannan zargi inda ta ba da tabbacin cewa za ta gudanar da bincike tare da daukar mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Ana zargin wasu jami’an hukumar yaki da sha fa fataucin kwayoyi (NDLEA) sun kashe wani matashi mai suna Faisal Yakubu Hussaini.

Ana zargin jami’an na NDLEA sun kashe Faisal Yakubu ne a garin Dangi, hedikwatar karamar hukumar Kanam a jihar Filato.

Kara karanta wannan

An kama riƙakƙun yan fashi da makami, sun sace kayan miliyoyi

Ana zargin jami'an NDLEA sun kashe wani matashi a jihar Filaton Arewacin Najeriya
Hukumar NDLEA ta yi martani yayin da aka zargi jami'anta da kashe wani matashi a Filato. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

An zargi jami'an NDLEA da kashe matashi

Mutanen garin sun ce lamarin ya faru ne yayin da jami’an suka kai samame a wani gidan saukar baki a yankin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an sun tsorata matashin da harbin bindiga inda har suka kashe shi a lokacin da ya ke cikin dimuwar harbin.

Al’ummar yankin sun kuma bayyana cewa sun yi tambayar ko wani laifi aka aikata a gidan saukar bakin amma jami’an ba su bayar da wata kwakkwarar amsa ba.

Shugaba da sakataren kungiyar cigaban Kanam (KADA), Barista G. Aliyu da ND Shehu Kanam, sun yi Allah wadai da wannan lamarin.

Al'umma sun yi tir da 'aikin' NDLEA

Sakataren ya ce:

"Shugabannin KADA sun yi matukar takaici da alhinin kashe Faisal Yakubu Hussaini Adafa da aka yi ba tare da bin ka’ida ba a Dengi, ranar 7 ga watan Nuwamba 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe bayin Allah ta hanya mai muni

"Yayin da muka yarda NDLEA na da hurumin gudanar da ayyuka bisa doron dokar kasa, hakan ba zai hana mu yi Allah wadai da wannan kasan kan ba.
"Muna kira ga hukumar NDLEA da ta kama tare da gurfanar da dukkanin jami’an da aka samu da hannu a wannan aika-aikar."

Kakakin hulda da jama’a na NDLEA a jihar, Abba Muhammad Sani, ya shaida cewa hukumar za ta binciki lamarin sannan ta dauki matakin da ya dace.

Matasa sun harbe jami'in NDLEA

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu matasa bata gari ne suka kwace bindigar a yankin Oruma a jihar Bayelsa daga hannun jami'an hukumar NDLEA.

Bayan sun kwace bindigar, matasan sun kubutar da wasu masu laifi guda biyu da aka kama kuma sun harbi jami'an NDLEA tare da ji wa wasu raunuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.