Ire Iren Ta'addancin da Sabuwar Kungiyar Lakurawa ke yi a Arewa

Ire Iren Ta'addancin da Sabuwar Kungiyar Lakurawa ke yi a Arewa

  • Hukumomin Najeriya sun tabbatar da samuwar sabuwar kungiyar yan ta'addan Lakurawa a wasu sassa na Sokoto da Kebbi
  • Mazauna wuraren da yan ta'addar ke zama sun bayyana yadda suka fara muzgunawa al'umma da ta'addancin da suke yi
  • An kuma bayyana cewa yan ta'addar suna amfani da yare da dama wajen yin magana; Fulatanci, Kanuri, Turanci da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Wasu mazauna jihar Sokoto sun bayyana yadda sabuwar kungiyar ta'addanci ta Lakurawa ke mu'amalantarsu.

An bayyana cewa Lakurawa na jingina da addini kuma suna yin horo na musamman ga duk wanda ya karya dokar da suke gani ta addini ce.

Kara karanta wannan

Sun sha wuta: Manyan yan bindiga sun fara neman mika wuya a ajiye makamai

Sokoto
Jerin ta'addancin da Lakurawa suka fara. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wani mazaunin Sokoto ya ce yan ta'addar na ikirarin kare kansu suke yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Lakurawa su ka hana aske gemu

Wani mazaunin Sokoto, Muhammadu Bauni ya bayyana cewa yan ta'addar suna dukan matasa idan su ka aske gemu ko suka ji waƙa.

Muhammadu Bauni ya kara da cewa Lakurawa na dukan duk wanda ya yi aski maras kyau amma har yanzu ba su fara garkuwa da mutane ba.

Abu mafi muni da Muhammadu Bauni ya ce suna yi shi ne jan hankulan matasa domin shiga tafiyarsu.

Lakurawa na yaki da ma'aikata

Wani mazaunin Sokoto ya ce Lakurawa na kashe ma'aikatan gwamnati kuma ya ce sun tafi da wani ma'aikacin lafiya da har yau ba a ji labarinsa ba.

Mutumin ya kara da cewa idan bako ya zo gari suna zuwa su dauke shi su yi masa tambayoyi, idan ba ma'aikaci ba ne, sai su kyale shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe bayin Allah ta hanya mai muni

'Yan Lakurawa na kai hari a Sokoto

An ruwaito cewa mafi yawan hare haren da ake kai wa kan jami'an tsaro a wasu yankunan Sokoto Lakurawa ne ke kai su.

Muhammadu Bauni ya ce sojoji sun taba zuwa garinsu suka kashe Lakurawa biyu amma daga nan ba su sake dawowa ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan ta'addar Lakurawa na jin Hausa, Fulani, Tuareg, Kanuri, Tuba da Turanci.

Sojojin Lakurawa na ba matasa kudi a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa sababbin yan ta'addar da aka sani da Lakurawa na rudan matasa a jihar Sokoto domin shiga tafiyarsu.

Wasu mazauna Sokoto sun tabbatar da cewa yan ta'addar suna ba matasa Naira miliyan daya domin su shiga kungiyar Lakurawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng