Gwamna a Arewa Zai Kashe N93bn a Samar da Ruwa, Zai Biya Ma'aikata Bashin N800m

Gwamna a Arewa Zai Kashe N93bn a Samar da Ruwa, Zai Biya Ma'aikata Bashin N800m

  • Gwamnatin Kaduna za ta kashe Naira biliyan 93 domin gyara bangaren ruwa da ya fuskanci kalubale a cikin shekaru 10
  • An ce gwamnatin za ta biya kudin ne a kashi kashi, inda ake ce za ta fara da biyan Naira biliyan 17 a wannan shekarar ta 2024
  • Gwamna Uba Sani ya kuma umarci a biya bashin Naira miliyan 800 da ma'aikatan kamfanin ruwan Kaduna (KADSWAC) ke bi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna na shirin kashe Naira biliyan 93 a cikin shekaru huɗu domin gyaran bangaren ruwa cikin rukunai huɗu.

Gwamnatin na da niyyar gyara bangaren ruwan domin magance tabarbarewar da wannan bangare ya fuskanta a shekaru 10 da suka gabata.

Kara karanta wannan

'Za mu gyara Najeriya,' Bukola Saraki ya fadi shirin da PDP ta yi na karbar mulki a 2027

Gwamnatin Kaduna ta yi magana kan gyara fannin ruwa a jihar
Gwamantin Kaduna za ta kashe N93bn wajen gyara fannin ruwa a jihar. Hoto: @Abdool85
Asali: Twitter

Kwamishinan ayyukan jama'a, Arc Ibrahim Hamza, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, kamar yadda Abdallah Yunus Abdallah ya ruwaito a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Kauduna zai biya ma'aikata bashin N800m

Abdallah Yunus Abdallah shi ne babban mataimaki na musamman kan sababbin kafafen watsa labarai ga Gwamnan Uba Sani.

“Gwamna Uba Sani ya bayar da umarnin biyan dukkanin albashin da ma’aikatan kamfanin ruwa na jihar Kaduna (KADSWAC) ke bi, wanda ya kai Naira miliyan 800.”

- A cewar kwamishinan ayyukan jama'a

Arc Hamza ya kuma bayyana cewa ma’aikatan KADSWAC za su ci gaba da samun albashi daga gwamnatin jihar har zuwa 2027.

A cewarsa, gwamnati na da yakinin zuwa 2027 kamfanin zai tsaya da kafafunsa tare da gudanar da ayyuka a matsayin kamfanin kasuwanci.

Gwamna zai kashe N93bn a gyara ruwa

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP ya jawo cire wasu manyan sakatarori a Kano? Gwamnati ta yi magana

Kwamishinan ya tuna cewa gwamnan ya taba sanya dokar ta-baci a bangaren ruwa, wanda ya kai ga nadin Injiniya Kabir Rufai a matsayin shugaban kamfanin KADSWAC.

A cewar kwamishinan, gwamnatin Kaduna na zuba jari sosai wajen gyara dukkanin cibiyoyin tace ruwa da hanyoyin rarraba ruwan ga fadin jihar.

Arc Hamza ya kuma bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 93 cikin rukunai hudu, za a fara da kashe Naira biliyan 17 a wannan shekarar.

Kwamishinan ya kara da cewa za a kashe Naira biliyan 35 a shekara mai zuwa, Naira biliyan 30 a 2026, sai kuma Naira biliyan 11 a 2027.

Gwamna Uba Sani ya amince da sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnati.

A yayin da gwamnatin tarayya ta amince da N70,000, shi gwamnan Kaduna ya amince da biyan N72,000 matsayin sabon albashin da zai fara aiki daga Nuwamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.