Yanzu-yanzu: An sa dokar ta baci a Kaduna, kowa ya zauna a gida

Yanzu-yanzu: An sa dokar ta baci a Kaduna, kowa ya zauna a gida

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar ta baci a fadin jihar saboda mutane sun sabawa dokokin farko da gwamnatin ta sanya domin hana shigowa da yaduwar cutar Coronavirus jihar.

Mataimakiyar gwamnan, Hadiza Balarabe, wacce ta sanar da hakan ranar Alhamis ta ce wannan shawara da aka yanke ya yi muwafaqa da kudin tsarin mulkin Najeriya.

A cewarta, kwamiti na musamman kan yakar cutar ta gana domin tattauna yadda cutar ke cin rayuka sauran jihohi da kasashen waje.

Tace: "Kwamitin ta samu rahoton cewa mutane sun sabawa dokokin hana taro a sanarwa daban-daban da tayi cikin kwanaki bakwai da suka wuce."

"An samu rahotonnin mutane sun yi ko oho da dokar hana hawa babur, Keken 'a daidaita sahu' , da motoci fiye da fasinjoji biyu a kujera da aka sanya."

"Saboda haka, daga daren Alhamis, 26 ga Maris 2020, wajibi ne dukkan mazauna jihar Kaduna su zauna a gida . Babu zuwa aiki, babu kasuwanci, babu zuwa wuraren ibada."

"Mutanen da aka amincewa fitowa kadai sune jami'an kwana-kwana, jami'an kiwon lafiya da jami'an tsaro."

"Za'a kulle Masallatai da cocuna, babu Sallar Jami'in da za'a amince a gudanar ciki ko waje."

"Duk wajen Ibada ko taron da aka kama ana taro, lallai sun saba doka kuma za'a iya kwace takardan mallakan filin wajen ko kuma kwace wajen."

Yanzu-yanzu: An sa dokar ta baci a Kaduna, kowa ya zauna a gida
Yanzu-yanzu: An sa dokar ta baci a Kaduna, kowa ya zauna a gida
Asali: UGC

KU KARANTA: Jigawa ta rufe iyakakokin ta da Bauchi, Kano da wasu jihohi biyu

Gabanin sanar wannan sabon dokar, Gwamnatin jihar Kaduna ta haramtawa babura masu kafa uku da aka fi sani da 'adaidaita sahu' da kananan motocin haya (taxi) jigilar mutane saboda basu cika ka'idar nesanta da ake bukata ba a yayin da ake fama da annobar cutar coronavirus.

Da take sanar da hakan a ranar Laraba, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe, an dauki wannan sabon matakin ne yayin wani taro da manyan jami'an gwamnatin jihar suka gudanar domin tattauna wa a kan matakan da aka dauka na dakile yaduwar kwayar cutar COVID-19.

Dakta Hadiza ta ce, ya zuwa yanzu ba a hana manyan motocin haya (bus) daukar fasinjoji ba, amma ba a yarda su dauki sama da mutum biyu ba a layin kujera daya ba a cikin motocinsu.

A cewarta, gwamnatin jihar a shirye take ta dakatar da duk wani nau'in sufuri a motocin haya idan yanayi ya nuna da akwai bukatar yin hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel