Bauchi: Kotu Ta Ɗauki Matakin Hukunta Tsohon da Ya Wallafa Hotunansa da Ƴan Mata

Bauchi: Kotu Ta Ɗauki Matakin Hukunta Tsohon da Ya Wallafa Hotunansa da Ƴan Mata

  • Bala Muhammed, dattijon nan na Bauchi da ya wallafa hotunansa da 'yan mata a shafin Facebook ya gurfana gaban kotu
  • Mai gabatar da kara, ASP Zakari Mohammed, ya shaida wa kotu cewa ana tuhumar Bala Muhammed da bata suna
  • Alkaliyar kotun, Misis Laraba Hamisu ta ba da umarnin tsare Bala Muhammed a gidan gyaran hali zuwa 27 ga Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bauchi - A ranar Alhamis ne 'yan sanda a Bauchi a suka gurfanar da wani dattijo mai shekara 76, Bala Mohammed, a gaban Kotun Majistare ta biyar.

An gurfanar da Bala Mohammed a gaban kotun ne bisa zargin ya wallafa hotunan mata da yawa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Lauyan yara da su ka yi zanga zanga ya fadi yadda gwamna Abba ya agaza masu

An gurfanar da Bala Muhammed a gaban kotu kan wallafa hotunan mata
Bauchi: Dattijon da ya wallafa hotunansa da 'yan mata ya gurfana a kotu.
Asali: Original

Tsohon da mazaunin rukunin gidaje Tambari ne a Bauchi na fuskantar tuhuma kan bata suna, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gurfanar da Bala a gaban kotu

Mai gabatar da kara, ASP Zakari Mohammed, ya shaida wa kotu cewa Bala Mohammed ya aikata laifin ne a cikin watan Oktoban 2024.

ASP Zakari ya bayyana cewa wanda ake zargi ya wallafa hotunan mata da yawa yana ikirarin cewa 'yan matansa ne kuma yana da alakar aure da su.

Wadda ta shigar da kara (da aka boye sunanta), ta bayyana cewa ta dauki hoto tare da wanda ake zargin ne kawai amma babu wata alaka tsakaninsu.

Kotu ta garkame Bala Muhammed

ASP Zakari ya bayyana cewa abin da Bala Mohammed ya aikata ya saba wa sassa na 183, 196, 388, da 389 na dokar laifuffuka ta jihar Bauchi (2022).

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa 3 da gwamnatin Tinubu ta fusata Mutanen Arewa da su

Alkaliyar kotun, Laraba Hamisu, ta bada umarnin tsare wanda ake zargi a gidan gyaran hali na Bauchi.

Mai shari'a Laraba Hamisu ta kuma dage shari'ar zuwa ranar 27 ga Nuwamba, 2024, domin ci gaba da bincike.

Hukumar Hisbah ta titsiye Bala Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Hisbah reshen jihar Bauchi ta yi wa Bala Muhammed tambayoyi kan wallafa hotunansa da 'yan mata a Facebook.

Titsiyewar da Hisbah ta yiwa dattijon na zuwa ne kwanaki bayan da hotunan Bala da 'yan matansa suka karade intanet tare da jawo ce-ce-ku-ce daga mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.