Lalacewar Tashar Wutar Lantarki: Ƴan Najeriya Sun Fusata, Sun Kira Tinubu

Lalacewar Tashar Wutar Lantarki: Ƴan Najeriya Sun Fusata, Sun Kira Tinubu

  • 'Yan Najeriya da dama sun mamaye kafafen sada zumunta domin nuna bacin ransu kan sake durkushewar tashar wutar lantarki
  • An ruwaito cewa, tashar wutar lantarkin ta sake lalacewa a karo na biyu cikin kwanaki uku, lamarin da ya jefa mutane a duhu
  • Bayan sanarwar durkushewar tashar da gwamnati ta fitar, Legit Hausa ta zanta da wasu 'yan Arewa, suka aika sako ga Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Da sanyin safiyar Alhamis, 7 ga Nuwamba ne kasuwanni da gidaje a Najeriya suka sake fuskantar daukewar wutar lantarki.

An rahoto cewa babbar tashar wutar lantarki ta kasa, ta durkushe a karo na biyu cikin kwanaki uku, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

Daga gyarawa, tushen wutar Najeriya ya kara lalacewa, kasa ta shiga duhu

'Yan Najeriya sun yi magana yayin da wutar lantarki ta sake lalacewa karo na 2
'Yan Najeriya sun aika sako ga Tinubu yayin da tashar wutar lantarki ta sake durkushewa. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tashar wutar lantarki ta sake lalacewa

Zuwa lokacin hada rahoton nan, kamfanin TCN bai fitar da wata sanarwa a dangane da lalacewar wutar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma shafin @NationalGridNg na X, mai ba da bayanai game da wutar lantarki a Najeriya ya tabbatar da hakan.

Shafin na @NationalGridNg ya rahoto cewa:

"An sake samun durkushewar tashar wutar lantarki."

'Yan Najeriya sun magantu kan lalacewar wuta

@Arakunrin_MFR:

"Da alama tashar wutar lantarki na da nau'in jinin SS ne tun da ba za ka mallaki lafiyayyen jini amma ka rika rashin lafiya kullum ba.
"Tashar wutar lantarki ta kasa na bukatar addu'ar 'yan kasa. Lallai sai an hada tashar da addu'a."

@jrnaib2 ya ce:

"Da alama dai mutanen nan suka marisa ne da irin halin da muke ciki."

Ana so Bola Tinubu ya gyara wuta

Kara karanta wannan

Kwamitin Tinubu ya farga da matsaloli 2 da ke jawo yawan lalacewar lantarki

A zantawarmu da Nura Haruna, wani mai sharhi kan lamuran yau da kullum a Funtua, jihar Katsina, ya ce akwai bukatar sshugaba Bola Tinubu ya gaggauta daukar mataki.

Nura Haruna ya yi nuni da cewa lalacewar wutar a kai a kai na iya zama cin fuska ga Najeriya a idon duniya, tare da jawo rashin kafuwar kamfanoni na waje.

Mai sharhi kan lamuran yau da kullum din ya ce akwai bukatar a samar da mafita ta din din din game da lalacewar wutar, domin gudun durkushewar tattalin arziki.

Tashar lantarki ta lalace karo na 10

Tun da fari, mun ruwaito cewa Najeriya ta sake fadawa cikin duhu yayin da aka rahoto cewa tashar wutar lantarki ta durkushe a ranar Talata, 5 ga Nuwamba.

Durkushewar tashar wutar ta ranar Talata ita ce karo na 10 da aka fuskanta a cikin shekarar 2024, lamarin da ya fara jefa ayar tambaya kan ingancin tashar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.