Mata Ta Karya Ɗan Kishiyarta da Taɓarya, Ta Zuba Masa Ruwan Zafi
- Wata kotu a jihar Enugu ta tura wata mata mai suna Ada Ogbogu gidan gyaran hali bisa zargin yi wa dan kishiyarta duka da taɓarya
- A yayin da aka gurfanar da Ada Ogbogu a kotu ranar Talata, dan sanda mai gabatar da kara ya ce laifin da ta aikata ya saba dokar kasa
- Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa bayan duka da taɓarya, matar ta zubawa yaron ruwan zafi wanda ya kara jefa shi cikin matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Enugu - Rundunar yan sanda ta tabbatar da kama wata mata da ake zargi ta karya yaro dan shekaru uku.
An ruwaito cewa matar ta yi wa yaron duka ne da taɓarya har ta kakkarya shi kuma ɗan kishiyarta ne.
Jaridar Vanguard ruwaito cewa gwamnatin jihar ta yi gargadi ga mutane masu cin zarafin ƙananan yara a Enugu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mata ta karya dan kishiyarta da taɓarya
A ranar Talata yan sanda suka gurfanar da wata mata mai suna Ada Ogbogu a wata kotun a jihar Enugu bisa zargin karya dan kishiyarta.
Ana zargin cewa Ada Ogbogu ta karya yaron dan shekaru uku ne bayan ta yi masa dukan tsiya da taɓarya kuma ta zuba masa ruwan zafi a hanci da baki.
Yan sanda sun tabbatar da cewa a ranar 23 ga watan Oktoba aka kama matar a unguwar Ani da ke yankin Enene a Enugu.
An tura Ada Ogbogu gidan gyaran hali
Bayan sauraron karar, alkalin kotun, mai shari'a Alphonsus Edeh ya bukaci a kulle ta a gidan gyaran hali.
Mai shari'a Alphonsus Edeh ya ce sai ranar 26 ga watan Nuwamba za a cigaba da sauraron karar kan zargin da ake yi wa Ada Ogbogu.
An hana belin Ada Ogbogu a kotu
This Day ta wallafa cewa biyo bayan tura matar da ake zargin kotu, lauyanta ya bukaci a bayar da belinta amma alkalin ya ki.
Kwamishinar jin kai ta jihar, Ngozi Enih ta tabbatar da cewa gwamnatin Enugu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta masu cin zarafin yara.
Mata ta kashe dan kishiyarta a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa kumar NAPTIP a jihar Kano ta kama wata mata bisa zargin yi wa dan kishiyarta duka har ta kai ga ya mutu.
Tun da farko, hukumar ta taba ceto yaron daga hannun matar ta ba shi kulawa, matar ta saka hannu kan takardar alkawarin za ta daina cin zarafinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng