Kano: 'Yan sanda sun kama matar da ta kashe ɗan kishiyarta

Kano: 'Yan sanda sun kama matar da ta kashe ɗan kishiyarta

- Hukumar NAPTIP a jihar Kano ta kama wata mata a Kano saboda laifin yi wa dan kishiyarta duka har ta kai ga ya mutu

- Tun da farko hukumar ta taba ceto yaron daga hannun matar ta bashi kulawa ta saka matar saka hannu kan takardar alkawarin za ta dena cin zarafinsa

- Sai dai bayan an mayar da yaron gida ta cigaba da galaza masa har sai da ya mutu, a halin yanzu an tura batun hannun rundunar 'yan sanda

An kama matar da ta kashe dan kishiyarta a Kano
An kama matar da ta kashe dan kishiyarta a Kano. Hoto daga The Guardian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bill Gates: Abinda Najeriya za ta yi don tsamo 'yan kasarta daga ƙangin talauci

Hukumar Hana Safarar Mutane ta Kasa, NAPTIP, a Kano ta kama wata matar aure mai shekaru 29, Jamila Abubakar kan kashe dan kishiyarta, Mohammed Bashir.

Kwamandan NAPTIP na Kano, Shehu Umar ya ce an kama wacce ake zargin ne a ranar Alhamis, bayan ta yi wa yaron duka har sai da ya mutu a kusa da kasuwar Tarauni a Kano.

Umar ya bayyana cewa hukumar ta taba gayyatar ta a baya a kan zargin cin zarafin yaron bayan an ceto shi daga wani daki da ta rufe shi a ciki ba tare da tana ba shi abinci ba.

KU KARANTA: An kama ɗan sanda bayan budurwarsa ta mutu a otel ɗin da suka kwana tare

Ya shaidawa kamfanin dillancin labarai, NAN, cewa NAPTIP ta samar ya yaron wurin zama da abinci da magunguna kafin aka mayar da shi hannun mahaifinsa bayan an bukaci iyayen su rattaba hannu kan yarjejeniyar cewa za su rika kula da shi.

Umar ya ce, "Amma abin takaici an cigaba da dukan yaron har sai da ya mutu, an sanar da rundunar 'yan sanda abinda ya faru domin su zurfafa bincike su kuma gurfanar da wanda aka samu da laifi a kotu."

A wani labarn daban, Isaac Ayodele wani tsohon ma'aikacin banki, a ranar Alhamis ya shaida wa alƙalin kotun gargajiya da ke a Mapo Ibadan cewa matarsa Omotayo ta yaudare shi ya siya babur daga hannun kwartonta.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa Ayodele ya kuma fada wa kotu cewa matarsa tana cin amanarsa na aure. "Na ce matata ta dena aiki bayan na samu aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164