'Yan Ta'adda Sun Hallaka Mutane 8 a Wani Harin Ta'addanci

'Yan Ta'adda Sun Hallaka Mutane 8 a Wani Harin Ta'addanci

  • Ƴan ta'adda sun yi ta'addanci a jihar Neja bayan sun kai wani hari kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Ana zargin cewa tsagerun sun hallaka mutane takwas ciki har da wasu mata guda biyu da suka ƙi yarda su yi lalata da su
  • Yan ta'addan da suka kawo harin a kan babura sun kuma ƙona gidaje masu yawa bayan sun kutsa cikinsu a ƙauyen Wayam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Ƴan ta'adda sun kashe wasu mata biyu a ƙauyen Wayam da ke Sabon-Gari a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Niger saboda ƙin yarda su yi lalata da su bayan sun kai hari.

Harin wanda ya auku a ranar Talata, ya kuma yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane takwas da ƴan ta’addan suka kashe yayin da aka ƙona gidaje da kayan abinci da dama.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun kashe bayin Allah ta hanya mai muni

'Ƴan ta'adda sun kai hari a Neja
'Yan ta'adda sun hallaka mutane takwas a Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Nation ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiya a lokacin da mutane ke ƙoƙarin fara harkokinsu na yau da kullum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan ta'adda sun kashe mutane a Neja

Rahotanni sun ce ƴan ta’addan sun shiga cikin ƙauyen ne a kan babura suna harbe-harbe yayin da wasu suka sauko suna ɓalle gidaje tare da ƙona su.

An kashe mutane biyar nan take ciki har da mata biyu da su ka ƙi amincewa su keta musu haddi. Ƴan ta'addan sun sare kawunansu sannan suka tafi da su.

Ƴan ta'addan sun kuma kashe wasu mutane biyar bayan sun harbe su da bindiga yayin harin.

Majiyoyi daga mutanen yankin sun ce waɗanda suka tsira daga harin sun bar ƙauyen saboda fargabar sake kai wani hari yayin da aka binne waɗanda aka kashe.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka kakaba harajin N150m kan mutanen kauyukan Zamfara

Ƴan sanda sun daƙile harin ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Imo ta sanar da samun nasarar ɗakile wani harin ƴan ta'adda a ranar Talata, 29 ga watan Oktoban 2024.

Rundunar ƴan sandan ta ce ta samu nasarar hallaka ɗaya daga cikin ƴan ta'addan waɗanda ake zargin na ƙungiyar IPOB/ESN ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng