Sojoji Sun Fadi Matakan da ake Dauka bayan Bullar Kungiyar Yan Ta'adda a Arewa

Sojoji Sun Fadi Matakan da ake Dauka bayan Bullar Kungiyar Yan Ta'adda a Arewa

  • Rundunar sojojin kasar nan ta tabbatar da shigowar sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda daga kasashen Mali da jamhuriyyar Nijar
  • Sanarwar da daraktan yada labaran rundunar, Edward Buba ta fitar ta ce yan ta’addan sun yi sansani a Kebbi da Sakkwato
  • Sanarwar ta ce rashin kwanciyar hankali ne ya samar da kungiyar a kasashen biyu kuma barazana ce ga Afrika ta yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da bullar sabuwar kungiyar yan ta’adda a jihohi biyu da ke Arewacin kasar nan.

Tabbacin rundunar ya zo bayan rahotanni sun bayyana bullar kungiyar yan ta’adda mai tsatstsauran ra’ayi da ake kira da lakurawa a Sakkwato.

Kara karanta wannan

Sabuwar kungiyar yan ta'adda na raba miliyoyi domin rudar matasan Arewa

Sojoji
Sojoji sun fara tabbatar da sabuwar kungiyar yan ta'adda Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

A wani sako da mai sharhi kan al’amuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X, rundunar sojojin kasar nan ta ce kungiyar yan ta’addan ta samu matsaguni a Kebbi da Sakkwato.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda kungiyar yan ta’adda ta zo Najeriya

Jaridar Daily Post ta tattaro cewa rundunar sojojin kasar nan ta ce sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda da ta shigo Najeriya na da alaka da kungiyoyi da ke ta’addanci a Mali da Nijar.

Daraka Janar kan harkokin yada labaran rundunar, Edward Buba ne ya tabbatar da haka, ya danganta lamarin da rashin zaman lafiya a kasashen biyu.

Abin da sojoji ke yi kan bullar yan ta’adda

A cewar sanarwar Edward Bubu, rundunar tsaron kasar nan na daukar wasu matakai bisa kungiyar yan ta’adda da ta shigo.

Ya ce hukumomin tsaron kasar nan su na sa ido a kan yadda kungiyar ke gudanar da aikinta, tare da shirin ko ta kwana kan duk wata barazana.

Kara karanta wannan

PDP ta fadi kullin da zai kori APC daga fagen siyasa bayan zaben 2027

Sabuwar kungiyar yan ta’adda ta bulla

A wani labarin kun ji cewa mazauna jihar Sakkwato sun shiga tsaka mai wuya bayan bullar sabuwar kungiyar yan ta’adda da ake yi wa lakabi da lakurawa da tuni su ka fara satar jama'a.

An samu rahoton cewa kungiyar ta samo asali ne daga rassanta da ke Mali, Nijar da Libya kuma yanzu haka sun ya da zango a dazuka da ke kananan hukumomi biyar a jihar Sakkwato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.