Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo Ya Yi Babban Rashi

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo Ya Yi Babban Rashi

  • Dan uwan tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Namadi Sambo ya rasu yana da shekaru 82 a duniya
  • Marigayiyin ya kasance yayan Namadi Sambo mai suna Alhaji Sulaiman Sambo, ya rasu bayan fama da jinya
  • Mutane da dama da suka halarci janazar sun yaba da irin halayen dattaku da yake da shi da gudunmawa da ya bayar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon mataimakin shugaban kasa a mulkin Goodluck Jonathan, Namadi Sambo ya yi rashin yayansa.

Marigayin mai suna Alhaji Sulaiman Sambo ya rasu a ranar Litinin 4 ga watan Nuwambar 2024 yana da shekaru 82 a duniya.

Yayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya rasu
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo ya yi rashin yayansa, Alhaji Sulaiman Sambo. Hoto: Namadi Sambo.
Asali: Facebook

Yayan Namadi Sambo ya kwanta dama

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, an bayyana dalilin Tinubu na sakin yaran Kano da aka kama

Vanguard ta ruwaito cewa marigayin kafin rasuwarsa ya bar mata daya da 'ya'ya 11 da jikoki 52 da tattaba kunne da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin rasuwarsa, marigayin ya yi aiki a tsohuwar ma'aikatar yada labarai a jihar Kaduna kusan shekaru 30 da suka wuce.

Alhaji Sambo mutum ne da ake mutuntawa a cikin al'umma kuma shugaban addini da ya bayar da gudummawa mai yawa.

Marigayin ya sha yabo daga al'umma kan dattaku

Mutane da dama a wurin jana'izarsa sun yaba da irin halayensa na kirki da kuma dattaku da yake da shi, Daily Post ta tabbatar a rahotonta.

Bayan gudanar da sallar jana'izarsa, an binne shi a makabartar Bashama da ke jihar Kaduna a Arewacin Najeriya.

Daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar akwai shi kansa Namadi Sambo da shugabannin addini da na siyasa da kuma yan uwa da abokan arziki.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun fadi dalilin Tinubu na sakin kananan yaran da aka kama

Matar tsohon hafsan tsaron Najeriya ta rasu

A baya, kun ji cewa an yi babban rashi bayan rasuwar matar tsohon hafsan tsaron Najeriya, Admiral Ola Sa'ad Ibrahim a birnin Tarayya Abuja.

Marigayiyar mai suna Aminat Dupe Ibrahim ta rasu ne a daren jiya Talata 5 ga watan Nuwambar 2024 bayan fama da gajeruwar jinya.

Hakan na zuwa ne bayan sanar da mutuwar hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja a jihar Lagos bayan fama da rashin lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.