An Yi Rashi: Hafsan Sojojin Kasan Najeriya Ya Rasu, Tinubu Ya Fitar da Jawabin Gaggawa

An Yi Rashi: Hafsan Sojojin Kasan Najeriya Ya Rasu, Tinubu Ya Fitar da Jawabin Gaggawa

  • An shiga jimami a Najeriya yayin da aka samu labarin rasuwar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, babban hafsan sojin kasa
  • Fadar shugaban kasa, ta hannun Bayo Onanuga, mai magana da yawun Bola Tinubu ta sanar da rasuwar a ranar Laraba
  • Sanarwar ta ce babban hafsan sojin kasan, Lagbaja ya rasu ne a daren ranar Talata a Legas bayan fama da rashin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da rasuwar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, babban hafsan sojin kasa.

Sanarwar da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaba Bola tinubu ya fitar ta ce Janar Taoreed Lagbaja ya rasu yana da shekaru 56.

Kara karanta wannan

An yi artabu: Sojoji sun kashe hatsabibin shugaban ƴan bindiga da yaransa a Arewa

Babban Hafsan sojin kasan Najeriya, Lagbaja ya rigamu gidan gaskiya
Fadar shugaban kasa ta sanar da rasuwar hafsan sojojin kasan Najeriya, Lagbaja. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Lagbaja: Hafson sojin Najeriya ya rasu

A sanarwar da ya fitar a shafinsa na X a safiyar Laraba, 6 ga watan Oktoba, Bayo Onanuga ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babban kwamandan sojojin kasa, na alhinin sanar da rasuwar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, babban hafsan sojin kasa, yana da shekaru 56.
"Ya rasu ne a daren ranar Talata a Legas bayan ya yi fama da rashin lafiya."

An rahoto cewa Laftanar Janar Lagbaja ya rasu ya bar matar sa Mariya da ‘ya’yansu biyu.

Tinubu ya aika sako bayan rasuwar Lagbaja

Laftanar Janar Lagbaja, wanda aka haifa a ranar 28 ga Fabrairu, 1968, ya samu mukamin hafsan soja a ranar 19 ga Yuni, 2023, ta hannun shugaba Tinubu.

A tsawon lokacin aikinsa, Janar Lagbaja ya nuna jagoranci na kwarai da jajircewa, inda ya yi aiki a matsayin kwamandan runduna ta 93 da kuma bataliya ta musamman ta 72.

Kara karanta wannan

Janar Lagbaja na cigaba da jinya, Tinubu ya karawa mukaddashin hafsan sojoji girma

Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan marigayin da sojojin Najeriya a wannan mawuyacin lokaci.

Shugaban kasar ya kuma yi wa Laftanar Janar Lagbaja addu'ar samun salama a kabarinsa tare da karrama gagarumar gudunmawar da ya baiwa al’umma.

Lagbaja na fama da rashin lafiya

Tun da fari, mun rahoto cewa hafsan sojojin Najeriya na fama da matsanancin rashin lafiya, inda har ake yada jita-jitar cewa ya tafi kasar waje jinya.

A yayin da aka ce Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja na kwance ba lafiya, majiyoyi sun shaida cewa wasu sojoji sun fara neman kujerarsa ta hafsan sojan kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labari

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.