An Yi Artabu: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Shugaban Ƴan Bindiga da Yaransa a Arewa

An Yi Artabu: Sojoji Sun Kashe Hatsabibin Shugaban Ƴan Bindiga da Yaransa a Arewa

  • Dakarun soji a karamar hukumar Wase da ke jihar Filato, sun kashe ‘yan bindiga biyar, ciki har da shugabansu, Kachalla Saleh
  • Kashe Kachalla Saleh na zuwa ne kasa da mako guda bayan wata arangama tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga a yankin
  • Abdullahi Haruna, dan banga kuma shugaban matasa a Wase, ya ce an kashe 'yan ta'addan a kauyen Kinashe, gundumar Bashar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Filato - Dakarun da ke aiki a sansanin ‘Operation Safe Haven’ a karamar hukumar Wase, jihar Filato sun kakkabe hatsabiban ‘yan bindiga.

An rahoto cewa dakarun sun kashe fitinannen shugaban 'yan bindiga, Kachalla Saleh da manyan yaransa hudu da suka addabi yankin.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ajalin 'yan ta'adda da ke kokarin hana gyara lantarkin Arewa

Sojoji sun halaka hatsabibin dan bindiga da yaransa hudu a Arewa
Sojoji sun kashe shugaban 'yan bindiga da yaransa a Filato. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Sojoji sun kashe shugaban 'yan bindiga

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an kashe Kachalla Saleh ne da misalin karfe 12 na rana a kauyen Kinashe da ke gundumar Bashar a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani dan banga kuma jagoran matasa a Wase, Abdullahi Haruna, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Jos a ranar Talata.

Abdullahi ya bayyana cewa jami’an tsaro sun dura kan ‘yan bindigar babu zato babu tsammani, suka kawo karshen barazanar Kachalla Saleh ga al'ummar yankin.

An jinjinawa sojoji kan kashe 'yan bindiga

Jaridar Daily Trust ta rahoto jagoran matasan ya yi bayani cewa:

“Yan bindiga sun kori mutane daga yankin, inda suka mayar da shi a matsayin mafaka. ‘Yan bindigar ba su yi tsammanin jami’an tsaro za su farmake su a lokacin ba."

Mazauna yankin Wase, musamman gundumar Bashar, sun yabawa sojojin bisa nasarar da suka samu ta kashe hatsabibin dan bindiga, Kachalla Saleh da yaransa.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa 3 da gwamnatin Tinubu ta fusata Mutanen Arewa da su

An ce kauyukan karamar hukumar Wase sun shafe shekaru suna fama da harin 'yan bindiga, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da jami’an tsaro.

'Yan banga sun gwabza da 'yan bindiga

Tun da fari, mun ruwaito cewa ‘yan bindiga da ’yan banga sun yi arangama a yankin Dogon Ruwa da ke karamar hukumar Wase, jihar Filato a makon jiya.

Aƙalla mutane huɗu ne suka rasu a arangamar da aka yi a yayin da 'yan ta'addan suka kai farmaki garin ne da niyyar yin garkuwa da mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.