Cyprus: Gwamnatin Zamfara Ta Magantu kan Halin da Dalibai Ke Ciki, Ta Soki Matawalle
- Gwamnatin Zamfara ta himmatu wurin shawo kan matsalolin da daliban jihar ke fama da su a kasar Cyprus
- Gwamnatin jihar ta ce za ta bi diddigi kan yadda aka dauki nauyin daliban 93 zuwa Cyprus a shekarar 2020
- Hakan ya biyo bayan shiga mugun yanayi da suka yi da aka yada a kafofin sadarwa wanda gwamnatin Bello Matawalle ta dauki nauyinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta nuna damuwa kan halin da dalibanta a kasar Cyprus suka shiga.
Gwamnatin ta ce tana iya bakin kokari wurin daidaita lamura kan daliban da gwamnatin Bello Matawalle ta dauki nauyi.
Zamfara za ta ɗauki mataki kan dalibanta a Cyprus
Kwamishinan yada labarai a jihar, Mallam Wadatau Madawaki shi ya bayyana haka a yau Talata 5 ga watan Nuwambar 2024, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Madawaki ya ce Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya himmatu wurin dakile matsalolin ɗaliban.
Ya jero matsalolin da daliban suka fuskanta inda ya bukaci yin bincike tare da yin adalci da bin diddigi.
"Wannan gwamnati ta mai girma Dauda Lawal ta himmatu wurin tabbatar da shawo kan matsalolin ɗaliban."
"Yana da matukar muhimmanci a yi bincike kan yadda aka dauki nauyin daliban zuwa ketare."
- Wadatau Madawaki
Madawaki ya ce Matawalle ya dauki nauyin dalibai 93 yan asalin jihar Zamfara zuwa ketare a shekarar 2020.
Ya zargi tsarin yadda aka dauki nauyin ɗaliban cikin rashin adalci da kuma tabbatar da gaskiya.
Har ila yau, ya ce daliban sun fara shiga matsaloli ne a 2022 lokacin da Matawalle ya bar tura musu kudi inda suka shiga mummunan yanayi.
Ƙungiya ta nemi afuwar Bello Matawalle
Kun ji cewa Ƙungiyar APC Akida Forum ta nesanta kanta da zanga-zangar da aka yi a ofishin EFCC domin neman a bincike Bello Matawalle.
Shugaban ƙungiyar a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa tuni suka kori mambobin da suka jagoranci zanga-zangar zuwa ofishin EFCC.
Ya bayyana cewa mambobin ƙungiyar da suka yi zanga-zangar kuɗi aka ba su domin su gudanar da aikin ba tare da bin ka'ida ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng