Gwamnatin jihar Zamfara ta tantance dalibai 200 da zata tura karatu kasashen waje
Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala tantance dalibai 200 da zata dauki nauyin tura su zuwa kasashen waje domin karo karatu.
Jagoran tsarin fitar da daliban zuwa kasashen waje, Dakta Jazuli Musa, ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Gusau yayin yi wa daliban bita wacce hukumar bayar da tallafin karatu a jihar ta shirya.
Musa ya ce daliban da gwamnatin za ta dauki nauyi zasu yi karatu ne a bangaren kiwon lafiya, kimiyyar na'ura mai kwakwalwa, injiniyarin da sauran su.
Ya ce za a tura 21 daga cikin daliban zuwa kasar China, 70 zuwa kasar India, 50 zuwa kasar Sudan yayin da ragowar 59 za a tura su zuwa kasar Cyprus.
DUBA WANNAN: Nasarar Buhari a Kotu: Gwamna Bello ya yi watsi da kudi, jama'a sun daka 'wawaso'
"Yanzu mun kammala tantance daliban, mu na musu bita ne kafin tafiyarsu.
"Mun samun a kalla mutane 700 da suka nuna sha'awar cin moriyar shirin, lamarin da yasa muka yi musu jarraba wa tare da tantance wa. Mun yi hakan ta hanyar hada gwuiwa da malamai a manyan makarantun jihar Zamfara," a cewarsa.
Lukman Majidadi, mai bawa gwamna shawara a kan harkokin da suka shafi bayar da tallafi ga dalibai, ya roki daliban su kasance wakilan jihar Zamfara nagari a kasashen da zasu je tare da mayar da hankali a karatu. (NAN)
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng