Babban Alkali a Najeriya da Ginin Kotu Ya Rufta Kansa Ya Rasu Yana da Shekaru 64
- Rahoto ya nuna cewa Allah ya karbi rayuwar babban alkalin Ekiti, Mai shari'a Oyewole Adeyeye bayan fama da rashin lafiya
- Duk da cewa ba a samu cikakken bayani game da rasuwar ba, amma majiyoyi sun shaida cewa alkalin ya rasu ne a safiyar Talata
- A shekarar da ta gabata ne aka rahoto cewa ginin babbar kotun jihar ya rufta kan marigayin a lokacin da ya ke aiki cikin ofishinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti - An shiga cikin tsananin jimami yayin da aka sanar da labarin rasuwar Mai shari’a Oyewole Adeyeye, babban alkalin jihar Ekiti.
Har yanzu dai ba a samu cikakken bayani game da rasuwar tasa ba, amma majiyoyi sun ce ya rasu ne a safiyar ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba.
Oyewole: Babban Alkalin jihar Ekiti ya rasu
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Mai shari’a Oyewole ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya ta sawon wata da watanni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Gwamna Kayode Fayemi ne ya rantsar da Mai shari'a Adeyeye a ranar 11 ga Oktoba, 2021.
A wata sanarwa da babbar magatakardar shari’a ta jihar Ekiti, Adegoke Olanike ta fitar, ta sanar da rasuwar babban alkalin wanda aka haifa a shekarar 1960.
An yi jimamin mutuwar alkalin Ekiti
A cikin sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ofishin magatakardar, Mista Oba Olayiwola Michael, Adegoke ta bayyana cewa:
"Marigayi babban alkalin ya kasance masanin shari’a mai daraja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da adalci da kuma daidaito."
“Gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban bangaren shari’a da jihar Ekiti gaba daya ba ta da iyaka kuma za a yi kewarsa."
Kungiyar mata lauyoyi ta kasa da kasa (FIDA) ta aika sakon ta'aziyya ga iyalai, 'yan uwa, ma'aikatar shari'a da ma jihar Ekiti kan wannan rashi, inji rahoton The Cable.
Gini ya fada kan Alkali Oyewole
A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai shari’a Adeyeye ya kwanta a asibiti bayan da wani sashe na babbar kotun jihar ya rufta masa a lokacin da yake cikin ofis.
Ba a samu asarar rai ba a yayin rugujewar ginin da ya afku a shekarar da ta gabata ba, amma rahotanni sun ce babban alkalin ya samu munanan raunuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng