Jastis Ibrahim Watila: Alkalin babbar kotun Nigeria ya rasu
- Jastis Ibrahim Watilan, alkali a babbar kotun gwamnatin tarayya reshen Abeokuta, ya rasu
- Wata sanarwa da ta fito daga kotun ta bayyana cewa Jastis Watila ya rasu ne ranar 24 ga watan Janairu, 2021
- Sanarwar ba ta bayyana sanadin mutuwar marigayi Jastis Watila ba
Alkali a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Jastis Ibrahim Watila, ya rasu.
Catherine Oby Nwandu, jami'in yada labarai na kotun, ta tabbatar da mutuwar Jastis Watila a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata.
Bayan bayyana cewa Jastis Watila, sanarwar ba ta ce uffan dangane da sanadin mutuwarsa ba.
"Babban alkalin manyan kotun Nigeria, Honarabul Jastis John Terhemba Tsoho, yana mai bakin cikin sanar da mutuwar Honarabul Jastis Ibrahim Watila, alkalin wannan kotu da ya rasu a ranar 24 ga watan Janairu, 2021.
KARANTA: Farfesa Jega ya amsa tambaya akan kokarin gwamnatin Buhari tun bayan hawa mulki
"Kafin rasuwarsa, Jastis Watila yana aiki ne reshen babbar kotun Nigeria da ke Abeokuta," a cewar wani bangare na sanarwar.
KARANTA: Katsina: 'Yan sanda sun yi caraf da Haruna Yusuf, jagoran safarar bindigu daga Nijar (Hoto)
Sanarwa ta bayyana cewa an haifi marigayi Jastis Watila a ranar 12 ga watan Mayu na shekarar 1963 sannan an fara nada shi alkali a babbar kotu a shekarar 2015.
Za'a yi jana'izarsa ranar Laraba, 27 ga watan Janairu, 2021 a gidansa da ke lamba C13 Herbert Macaulay a rukunin gidajen Pent da ke Pyakkasa da misalin karfe uku na rana.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmed Umaru Fintiri, ya nuna juyayi tare da bayyana alhinin rasuwar jigo a jam'iyyar PDP, Alhaji Ahmed Song.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa marigayi Ahmed ya rasu ranar Talata, 12 ga watan Janairu, 2021, yana da shekaru 75 a duniya.
A sakonsa na ta'aziyya, gwamna Fintiri ya bayyana cewa rasuwar Alhaji Ahmed babban rashi ne da ya girgiza shi.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng