Sanatocin Arewa Sun Fadi Dalilin Tinubu na Sakin Kananan Yaran da aka Kama
- Kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya sun ce shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi kokari da ya bayar da umarnin sakin yaran da aka kai kotu
- Gwamnatin Tinubu na shari’a da yaran ne bisa zargin sun daga tutar Rasha a lokacin zanga zangar adawa da yunwa a Kano da wasu jihohin
- Amma ko da aka gurfanar da yaran a gaban kotu a birnin Abuja, an ga alamun yunwa a tattare da su har wadansu daga cikinsu sun suma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Sanatocin tarayyar Najeriya da su ka fito daga Arewacin kasar sun jinjinawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Yabon ya zo a gabar da shugaban ya bayar da umarnin a saki dukkanin yara da ake tsare da su saboda zanga-zangar #EndBadGovernance.
Channels Television ta wallafa cewa kungiyar Sanatocin karkashin shugabanta, Abdulaziz Musa Yar’adua ta ce shugaba Bola Tinubu ya yi abin da ya dace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Tinubu ya damu da al’umma” - Sanatocin Arewa
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Sanatocin Arewa sun ce matakin da shugaba Tinubu ya dauka a kan yaran da gwamnatinsa ta tsare ya nuna dattakonsa.
Kungiyar ta ce umarnin sakin yaran ya kara tabbatar da yadda gwamnatin tarayya ta damu da kare hakkin matasa a fadin kasar nan.
Sanatocin Arewa sun yabi jagororin yankin
Sanarwar da kungiyar Sanatocin Arewa ta fitar ta bayyana jin dadi bisa yadda shugabanni a shiyyarsu su ka jajirce kan sakin yaran da gwamnati ta tsare.
An gurfanar da yaran a gaban babbar kotun tarayya, inda aka ga alamun yunwa a tattare da su har ta kai wasu daga cikinsu sun suma.
Matasan Arewa sun fusata da Tinubu
A baya mun ruwaito cewa kungiyar matasan Arewa ta ‘North Youth Alliance’ ta ce matakin da gwamnati ta dauka na kama tare da tsare kananan yara ya saba ka’ida kuma an tauye masu hakki.
Shugaban kungiyar, Aliyu Bin Abbas a madadin wasu kungiyoyin matasan Arewa da ke jihohi 19 na shiyyar sun bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta sakin yaran tare da daina tuhumarsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng