Gwamnati Ta Bayyana yadda Barayi Suka Sace Ganga Miliyan 8 na Danyen Mai a 2023

Gwamnati Ta Bayyana yadda Barayi Suka Sace Ganga Miliyan 8 na Danyen Mai a 2023

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a cikin shekarar 2023, Najeriya ta yi asarar kimanin gangunandanyen mai miliyan 7.68
  • Ta bakin hukumar NEITI, gwamnatin ta koka kan yadda aka samu karuwar satar mai da 79% a 2023 idan aka kwatanta da 2022
  • Shugaban hukumarNEITI, yayin wani taro a Abuja, ya nemi hadin kan kungiyoyin fararen hula wajen inganta ayyukan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban hukumar NEITI, Dakta Orji Ogbonnaya Orji, ya ce an sace ko kuma an yi asarar kimanin ganga miliyan 7.68 na danyen mai a shekarar 2023.

Dakta Orji ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bude taron kungiyar farar hula na kwanaki uku kan tsarin NEITI a Abuja.

Kara karanta wannan

Dillalan mai 4 sun shigo da fetur na N833bn yayin da Dangote ya fadi farashinsa

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan man da Najeriya ta yi asara a 2023.
Gwamnatin tarayya ta ce Najeriya ta yi asarar ganga miliyan 7.68 na mai a 2023 Hoto: @business
Asali: Getty Images

Najeriya ta yi asarar ganguna miliyan 7.68

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban NEITI ya gabatar da makala mai taken: 'Ayyukan NEITI da tasirin kungiyoyin farar hula wajen samar da shugabanci na-gari.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Orji ya ce:

"Rahoton NEITI ya nuna cewa a shekarar 2023, an sace kusan ganga miliyan 7.68 na danyen mai ko kuma an yi asararsa, kusan kashi 79 idan aka kwatanta da alkaluman 2022."

Ya karfafa gwiwar kungiyoyin fararen hula da su sanya ido kan dabarun gwamnati na yaki da satar danyen mai tare da bayar da shawarwari domin kare muhalli.

Game da asarar kudaden shiga da rashin bayar da rahoto, Jaridar The Nation ta rahoto Dakta Orji ya ce:

"Rahoton ya bayyana cewa kudin shiga da gwamnatin tarayya ya kamata ta samu sun kai sama da dala biliyan 6.071 da kuma Naira biliyan 66.4."

Kara karanta wannan

Yadda Hadiza Bala Usman ta samu wuka da nama wajen yanka ministocin Tinubu

Gwamnati ta ba kungiyoyi shawarwari

Dangane da janye tallafin man fetur da gyare-gyare a bangaren man, Dakta Orji ya bukaci kungiyoyin da su tabbatar da cewa kudaden tallafin sun isa ga ayyukan raya kasa.

Game da tasirin muhalli da matsalolinsu, Dakta Orji ya yi kira ga ƙungiyoyin da su ba da shawarwari na ƙarin kariya da dorewar muhallan, musamman a yankin Neja Delta.

Dangane da batun sauyin makamashi da na yanayi, Dakta Orji ya ce kungiyoyi na da muhimmiyar rawa wajen samar da sauyin da ba zai yi illa ga al'ummomi masu rauni ba.

Najeriya na asarar N1.29tr duk shekara

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce Najeriya na asarar Naira tiriliyan 1.29 a duk shekara sakamakon satar mai da sauran laifuffuka.

Abbas Tajudeen ya bayyana cewa Najeriya tana asarar kusan gangar ɗanyen mai 300,000 kowace rana wanda ya jawo kullum kasar ke tafka asarar miliyoyin kudin shiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.