Kano: Likitoci Sun Dauki Zafi, Sun ba Gwamna Awanni 48 Ya Kori Kwamishiniyarsa
- Kungiyar NMA ta kafe a kan lallai sai gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sallami kwamishiniyarsa daga aiki nan da kwanaki biyu
- Shugaban NMA reshen jihar Kano, Dr. Abdurrahman Ali ya shaidawa Legit cewa ana zargin kwamishiniya Amina Abdullahi da cin zarafi
- Ya kara da cewa kwamishiniyar da ke kula da ma'aikatar jin kai da walwala ta kai matasa da makamai asibitin Murtala don barazana da likita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Kungiyar likitoci ta kasa (NMA), reshen Kano ta ba gwamnatin jihar wa'adin awanni 48 ta kori kwamishiniyar walwala da jin kai, Hajiya Amina Abdullahi.
Kungiyar NMA ta zargi Amina Abdullahi da aka fi sani da Amina HOD da cin zarafin wata likita a lokacin da ta ke tsaka da aikin kula da marasa lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NMA na Kano, Dr. Abdurrahman Ali ya shaidawa Legit cewa su na zargin Amina HOD da cin zarafin Dr. Nusaiba Mahmud a bakin aikinta.
NMA ta zargi kwamishiniyar da cin zarafi
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Dr. Nusaiba Mahmud na tsaka da aiki a bangaren yara na asibitin Murtala a ranar Jumu’ar da ta gabata lokacin da Amina HOD ta iso asibitin.
Shugaban NMA na Kano, Dr. Abdurrahman Ali ya ce lokacin da aka shaidawa kwamishiniyar cewa babu maganin da ta zo nema, sai ta dauko yara da makamai ana yi wa likitan barazana.
Kungiyar NMA ta nemi Abba ya kori kwamishiniyarsa
Sanarwar da kungiyar NMA ta fitar ta ce Amina HOD ta fadi kalamai marasa dadi, ciki har da rashin ladabi ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Likitocin na ganin rayuwar jama'a na cikin barazana matukar gwamnan Kano bai sallame ta, tare da dora wanda ta dace da rike mukamin ba.
Gwamnatin Abba za ta shiga batun daure yara
A baya kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyarta na shiga batun yara kanana da gwamnatin Bola Tinubu ta daure domin a samu dawowa da su gaban iyayensu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka bayan bidiyon mawuyacin halin da yaran ke ciki ya bayyana a kotu, tare da cewa tuni aka fara daukar matakin kubuto da yaran zuwa gida.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng