Gwamnati Ta Yi Martani ga Atiku, Ta Fadi Abin da zai Faru Idan da PDP ke Mulki
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi martani ga kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar bisa tsare-tsarenta
- Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya yi magana a sanarwar da ya fitar a daren Lahadi
- Ya zargi Atiku da cika baki, domin a cewarsa wasu daga cikin manufofin tsohon dan takarar na daga cikin dalilan faduwarsa zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki zafi bayan tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki matakan da ta dauka kan tattalin arziki.
Fadar shugaban kasa ta ce babu dalilin da Atiku Abubakar zai rika kwatanta matakan gwamnati da kudurinsa wanda babu wanda ya taba gwadasu ballatana a gano amfaninsu.
A sanarwar da hadimin shugaba Tinubu kan kafafen yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Atiku Abubakar ba zai iya mulkin Najeriya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu ta caccaki Atiku Abubakar
Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnatin tarayya ta bayyana cewa 'yan Najeriya ne da kansu su ka nuna rashin gamsuwa da tsare-tsaren Atiku Abubakar.
A martani ga Atiku da Bayo Onanuga ya fitar, ya ce daya daga cikin dalilan da ya fadi zaben 2023 shi ne batun cefanar da kamfanin mai na kasa (NNPCL).
"Atiku zai jefa Najeriya a wahala;" Gwamnati
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa da Atiku Abubakar ne ya ke mulkin Najeriya, tuni yan kasar nan sun fada bakin talaucin da ya fi wanda ake ciki a yanzu.
Gwamnati ta ce ko a harkar ilimi, an ga yadda Atiku Abubakar a lokacin da ya ke rike da mukamin mataimakin shugaban kasa su ka gina jami'o'in kansa a maimakon gyara ilimin kasa.
Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu
A wani labarin mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gurfanar da yara masu karancin shekaru gaban kotu.
Atiku Abubakar ya ce gwamnatin tarayya ta nuna rashin tausayi yayin da aka gurfanar da yaran a gaban kotu saboda adawa da manufofin da Bola Ahmed Tinubu ya zo da su a kan tattalin arziki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng