An Kawo Dabarar Tunawa da Mutane 180 da Tankar Fetur Ta Kona Har Abada a Jigawa
- Gwamnatin Umar Namadi ta saye jami’ar Khadijah da ke garin Majia, yanzu ya zama mallakar al’ummar Jigawa
- Ba a dade da yin haka ba sai mutane suka mutu da wata tankar man fetur ta yi hadari a karamar hukumar Taura
- Shamsu Sa’id ya yi rubutu, a nan ya yi kira ga gwamnan Jigawa ya canza sunan jami’ar Khadijah zuwa October 15
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Jigawa - Kwanakin baya wata mummunar jarrabawa ta aukawa mutanen jihar Jigawa, tankar man fetur ta kashe mutane da yawa.
Wata mota da ta dauko fetur ta yi hadari a garin Majia, mutane da yawa da suka zo diban mai sun gamu da ajalinsu a cikin duhu dare.
Jami'a za ta tuna da hadarin Jigawa
A wani rubutu da ya yi a shafin Facebook a watan Oktoba, wani Shamsu Sa’id ya yi kira ga gwamnatin Jigawa a dalilin abin da ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malam Shamsu Sa’id ya roki gwamnatin Umar Namadi ta canza sunan jami’ar Khadijah University, Majia zuwa jami’ar October 15.
Matashin yake cewa idan aka canza sunan makarantar, watakila ba za a taba mantawa da wadannan mutanen Majia da suka rasu ba.
Kamar yadda ya yi bayani a rubutunsa, ko nan da shekaru 100 ne, idan sunan jami’ar ta nan, ba za a iya mantawa da labarin mamatan ba.
Shawara zuwa ga gwamnan jihar Jigawa
A maimakon gwamnatin Umar Namadi ta yi ta rabawa iyalan wadanda suka mutu shinkafa kurum, Sa’id ya na ganin hakan zai fi dacewa.
A shekarun baya, ya ce an radawa wata jami’a a kasar Masar irin sunar nan da aka gamu da makamancin wannan kaddara a lokacin.
Bayan haka, ya kawo shawarar kafa wata gidauniya da za ta dauki nauyin karatun iyalan da wadanda suka rasu a watan jiya suka bari.
Idan dai aka yi haka, ya ce ba za a samu wani maraya daga cikin gidajen mamatan da zai rasa hanyar da zai samu karatun zamani ba.
"IBTILA'IN MAJIA
"CANZA SUNAN KHADIJA UNIVERSITY MAJIA, ZUWA OCTOBER 15 UNIVERSITY, MAJIA (O15UM)
"Ina kira ga Gwamna da ya can sunan sabuwan jamiar da za'a bude ta Khadija University, Majia zuwa sunan Ranar da IBTILA'IN gobarar nan ya faru domin tunawa na har abada.
A sa mata suna Misalin: OCTOBER 15 UNIVERSITY, MAJIA.
-
Gwamnatin Jigawa za ta yi koyi da Masar?
"Irin wannan ba sabon suna ba ne, a qasar Masar Egypt akwai Jamia Mai suna kusan haka October 6 University
"Yin hakan zai sa ake tunawa da alhinin mutane 170 da suka rasu nan da shekara 30-100.
"Wani zai tambaya, me yasa aka sawa wannan Jamia suna haka?"
Gwamnatin Jigawa ta saye jami'ar Khadija
A can kwanakin baya, Legit ta rahoto cewa gwamna Umar Namadi ya amince da sayen jami'ar kuɗi ta dawo hannun gwamnatin Jigawa.
Gwamnatin Jigawa ta kafa kwamitoci da za su ba ta shawari kan saye da gyara jami'ar Khadija da ke Majia domin talakawa su amfana.
Asali: Legit.ng