Babban 'Dan Siyasa Ya Fadi Minista 1 Mai Kokari a Gwamnati da Tinubu Ya Sallama
- Dr. Aliyu Usman Tilde ya yi gajeren tsokaci ‘yan kwanaki kadan da jin Bola Tinubu ya sauke wasu ministocinsa
- Tsohon kwamishinan ilmin Bauchi ya yi magana ne game da Tahir Mamman da ya rasa kujerar ministan tarayya
- Tilde ya yi ikirarin cewa Farfesan ya na cikin wadanda suka fi kokari a cikin ministocin da aka nada a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Aliyu Usman Tilde ya na cikin wadanda ke tare da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kuma ya saba sharhi a kan al’amura.
Aliyu Usman Tilde ya yi magana da ya samu labarin Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya sallami wasu daga cikin ministocinsa.
Tahir Mamman ya bar matsayin minista
A maganar da ya yi a shafinsa na Facebook, tsohon kwamishinan na ilmi ya kare wani daga cikin ministocin da aka fatattaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aliyu Usman Tilde ya wanke Farfesa Tahir Mamman SAN daga zargi kwanaki kadan da rasa kujerarsa na babban minista na ilmi.
Tsohon kwamishinan na ilmin jihar Bauchi yake cewa bai kamata a bata mutane saboda kurum an yi waje da su a gwamnati ba.
Dr. Aliyu Tilde wanda shi kan shi ya san harkar ilmi ya ce Farfesan watau Tahir Mamman ya na cikin wadanda suka fi kokari a ofis.
A ra’ayinsa, idan ana maganar ministocin da suka fi kwazo a gwamnatin Bola Tinubu, Farfesa Tahir Mamman yana sahun gaba.
Tilde ya na ganin cewa siyasa ce kurum ta shafi kwararren lauyan har ta kai shugaban kasa ya kore shi da ya tashi garambawul.
Aliyu Tilde ya yabi tsohon ministan ilmi
"PROF TAHIR MAMMAN
Bai kamata mu bata mutane saboda kurum an yi waje da su daga mukami ba.
Mukaman siyasa haka su ke. Farfesa ya na cikin wadanda suka fi kowa a gwamnatin."
Korar Ministan ilmi ya jawo maganganu
Wasu da suke martani a shafin tsohon malamin sun yi ikirarin Hadiza Bala Usman ta yaba da kokarin Tilde a ma’aikatar harkar ilmi.
A cewarsu yunkurin yakar masu digirin bogi daga kasashen Afrika da haramtawa kananan yara shiga jami’a ne ya taba Mamman.
Wasu kuma sun yaba da yadda ya taka rawar gani wajen ganin ya wareware sabanin kungiyar ASUU da kuma gwamnatin tarayya.
Minista zai karbi batun shari'ar yara 76
Labari ya gabata cewa Ministan shari’a ya samu labarin an gurfanar da kananan yara a kotu saboda zanga-zanga da aka yi kwanaki.
Babban lauyan gwamnatin Bola Tinubu ya yi umarni a kawo masa takardun shari’ar da ake yi a kotun Abuja bayan an yi ta surutu.
Asali: Legit.ng