Kamfanin BUA bai Jin Gari, Ya Samu Naira Tiriliyan 1.07 a cikin Watanni 9 a 2024

Kamfanin BUA bai Jin Gari, Ya Samu Naira Tiriliyan 1.07 a cikin Watanni 9 a 2024

  • Kamfanin BUA foods Plc ya samu cinikin Naira tiriliyan 1.07 a cikin watanni tara na shekarar 2024 mai karewa
  • A rahoton da kamfanin ya fitar, ribar da aka samu a bana ta haura ta shekarar 2023 da aka samu N524.42bn
  • Kamfanin ya samu gwaggwaɓar ribar a lokacin da ƴan ƙasar nan ke cewa da ƙyar su ke iya sayen kayan abinci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kamfanin BUA foods Plc ya fitar da bayanin cinikin da ya samu a cikin watanni tara, wanda ya fara daga watan Janairu zuwa Satumba 2024.

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su fuskanci matsala, za a samu jinkirin albashin wasu watanni

Rahoton ya nuna yadda BUA ya samu cinikin Naira tiriliiyan 1.07 duk da ƴan ƙasa da ke sayen kayayyakin na cikin matsanancin talauci.

Kamfani
BUA ya yi cinikin N1.07trn a 2023 Hoto: BUA Group
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kamfanin ya samu gagarumar riba fiye da shekarar 2023 da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ribar kamfanin BUA ta ƙaru

Rukunin kamfanin BUA da ya haɗa da reshensa da ke samar da taliya, fulawa, shinkafa, semolina da sukari ya samu karin 104% na ciniki a 2024.

Rahoton PM News ta tattaro cewa wannan na ƙunshe a cikin rahoton kuɗin da kamfanin ya samu gabanin cire haraji na watanni tara.

Ribar kamfanin BUA ya haura na 2023

Cinikin da kamfanin BUA ya samu daga sayar da kayan abinci da mazauna kasar na ke iya saye da ƙyar ya haura na 2023 da ta samu N524.42b.

Ribar da kamfanin ya samu bayan biyan haraji ya ninka na bara da 91% inda ya N201.38bn idan aka kwatanta da 2023 da ya samu N105.61bn.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun fusata, sun gayyaci shugaban NNPCL kan matsalar fetur

Kamfanin BUA ya fadi dalilin tsadar abinci

A baya mun ruwaito cewa shugaban kamfanin Buga, Alhaji AbdulSamad Rabi'u ya fallasa wadanda ke jawo tsadar farashin kayan abinci a kasuwannin kasar nan.

Alhaji AbdulSamad Rabi'u ya ɗora alhakin matsalar tsada da ake samu a kan abokan hulɗarsu, musamman yan kasuwa da ƙara akalla N20,000 a kan kowane buhun fulawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.