Gwamnoni Sun Bukaci Sanatocin Arewa Su yi Watsi da Wata Buƙatar Tinubu
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi karin haske kan wasu abubuwa da suka tattauna yayin taron gwamnonin Arewa
- Dauda Lawal ya bayyana matakin da suka dauka wajen ganin dokar haraji ta Bola Tinubu ba ta samu nasara a majalisa ba
- Haka zalika gwamna Dauda ya yi bayani kan halin da ake ciki kan rashin tsaro a Zamfara bayan shafe shekaru ana fama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara ya yi karin haske kan dokar haraji da shugaba Bola Tinubu ke son tabbatarwa.
Dauda Lawal ya fadi dalilin da ya sanya gwamnonin Arewa adawa da sabuwar dokar tsarin haraji a Najeriya.
Gwamnan ya yi bayani ne a wata hira da ya yi da RFI Hausa kamar yadda ta wallafa bidiyon a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatoci za su yi watsi da bukatar Tinubu
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa dukkan gwamnonin Arewa sun nuna kin amincewa da sabuwar dokar haraji ta Bola Tinubu.
A karkashin haka, gwamnan ya ce sun yi umarni ga dukkan Sanatoci da yan majlisar wakilan Arewa su ki amincewa da dokar idan aka kawo ta majalisa.
Gwamnan ya ce suna da tabbacin cewa dokar za ta cutar da al'ummar Arewa kuma saboda haka ne suka juya mata baya.
Tsaro: Halin da ake ciki a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa a halin yanzu an samu cigaba sosai a kan yadda ake yaki da yan bindiga a jihar Zamfara.
Dauda Lawal ya kara da cewa a baya ana jin labarin an kashe mutane sama da 100 ko 200 a Zamfara amma a yanzu haka labarin ya sauya.
Sai dai duk da nasarar da ake samu, Dauda Lawal ya ce za a dauki lokaci kafin a samu cikakkiyar nasara a kan yan bindiga a jihar.
Gwamnati za ta saka sola a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa rashin wutar lantarki ya sanya gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu neman mafita a jihohin Arewacin Najeriya.
Ministan wuta, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa a yanzu haka an fara ƙoƙarin samar da wutar lantarki da hasken rana a Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng