Kasar Waje Ta Fara Harin Fetur daga Matatar Dangote a Najeriya
- Kasar Ghana ta bayyana cewa ta na duba yiwuwar fara dakon man fetur daga matatar Dangote maimakon daga Turai kamar yadda ta saba
- Shugaban hukumar kula da sha’anin man fetur na Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ne ya bayyana haka a wani taro da ya gudana a Legas
- Ghana ta nuna sha’awar sayen fetur daga Najeriya a lokacin da ake ta samun nakasu wajen fara sayarwa da yan kasar fetur daga matatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Alamu sun nuna cewa kasar Ghana na shirin fara jigilar fetur daga matatar Dangote da ke jihar Legas zuwa kasar ta.
Wannan na zuwa a lokacin da aka gaza cimma matsaya kan sayarwa jama’ar kasar nan man fetur da kamfanin matatar Dangote ke tacewa a kullum.
Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban hukumar kula da sha’anin man fetur na kasar Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ya bayyana yiwuwar fara sayen fetur daga matatar Dangote.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ghana na son sayen fetur daga Dangote
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kasar Ghana na shirin watsi da sayo fetur daga Turai inda ta ke kashe akalla $400m a kowane wata.
Shugaban hukumar da ke kula fetur na Ghana, Mustapha Abdul-Hamid ne ya fadi haka a wani taro da ya gudana a jihar Legas.
Mustapha Abdul-Hamid na wannan batu ne yayin da matatar Dangote ta fara fitar da fetur tun ranar 15 Satumba, 2024.
“Fetur zai yi yawa:” Ghana
Kasar Ghana ta ce da zarar matatar Dangote ta fara fitar da gangar fetur 650,000 a kowace rana, mai zai yi wa Najeriya yawa matuka.
Ghana na ganin maimakon ta ci gaba da sayo fetur daga Rotterdam daga Turai, za ta fara dauko fetur daga Najeriya a maimakon daukowa daga kasashen waje.
Matatar Dangote ta zauna da yan kasuwa
A baya mun ruwaito cewa yan kasuwar man fetur a Najeriya su na tattaunawa da matatar Dangote domin ganin yadda za su fara sayen fetur kai tsaye daga kamfanin maimakon daukowa daga kasar waje.
Tun bayan janyewar kamfanin mai na kasa (NNPCL) daga shiga tsakanin yan kasuwar man fetur na kasar nan da matatar, wanda ake sa ran haka zai taimaka wajen rage tsadar man fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng