'Ku Kara Hakuri': Gwamnati Ta Bayyana Inda Aka Kwana Game da Gyaran Wutar Arewa

'Ku Kara Hakuri': Gwamnati Ta Bayyana Inda Aka Kwana Game da Gyaran Wutar Arewa

  • A yayin da aka shafe kusan mako guda ba tare da wutar lantarki a wasu jihohin Arewacin Najeriya ba, TCN ya yi bayani
  • Kamfanin TCN ya bayyana cewa ya hada kai da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro domin gyara wutar
  • TCN ya ce 'yan ta'adda ne suka lalata layin wuta na Shiroro zuwa Kaduna, amma nan ba da dadewa ba injiniyoyi za su gyara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin wutar lantarkin Najeriya (TCN) ya ce yana kan daukar matakai domin gyara wutar da ta lalace daga Shiroro zuwa Kaduna.

Lalacewar layin wutar Shiroro ya janyo an samu daukewar wutar lantarki a Kaduna, Kano da sauran manyan biranen arewacin kasar, a cewar TCN.

Kara karanta wannan

Lalacewar wuta: Atiku ya dauki zafi kan lamarin, ya kawo hanyar dakile matsalar

Kamfanin TCN ya sake yin magana kan halin da wutar Arewa ke ciki
Kamfanin TCN ya hada kai da ofishin Nuhu Ribadu domin gyara wutar Arewa. Hoto: Anton Petrus
Asali: Getty Images

Matakan da TCN ya dauka na gyara wuta

Kamfanin TCN ya ce ya hada kai da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro domin gyara layin wutar da ya lalace, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da manajar hulda da jama’a ta TCN, Ndidi Mbah ta fitar, ta ce TCN na aiki tukuru domin gyara wutar cikin gaggawa duk da kalubalen tsaro da ake fuskanta.

"Injiniya (Misis) Nafisatu Ali, a wani jawabi da ta yi, ta ce mahara sun lalata layin Shiroro zuwa Kaduna wanda ke samar da wutar lantarki ga Arewacin Najeriya.
"A martani kan hakan, TCN ta hada gwiwa da ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro domin tabbatar da tsaron yankin, tare da ba injiniyoyi damar gyara matsalar."

- A cewar sanarwar.

Abin da ya jawo lalacewar wutar Arewa

Kara karanta wannan

'Abin takaici ne': Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan kiran juyin mulki, ta yi gargadi

Misis Mbah ta jaddada cewa rashin wutar da ake fama da shi a jihohin Arewa na kwanakin nan ya samo asali ne sakamakon lalata layin Shiroro zuwa Mando da aka yi.

Ta kara da cewa rashin tsaro a yankin Arewa ya kawo tsaiko wajen gyaran da ake bukata domin maido da wadatacciyar wutar lantarki.
“Mun tsaya tsayin daka wajen ganin mun shawo kan wadannan kalubale saboda mun fahimci matsayin wutar lantarki a rayuwar al’umma da tattalin arziki."

- A cewar sanarwar Misis Mbah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.