Gwamna Radda Ya Yunkuro, Ya Faɗi Abin da Zai Biya a Matsayin Mafi Karancin Albashi

Gwamna Radda Ya Yunkuro, Ya Faɗi Abin da Zai Biya a Matsayin Mafi Karancin Albashi

  • Gwamnatin Katsina ta amince za ta fara biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa watau N70,000
  • Gwamnatin karƙashin Gwamna Dikko Raɗɗa ta kafa kwamitin mutum 15 da zai tsara yadda za a yi wa ma'aikata ƙarin albashi a kowane mataki
  • Mataimakin gwamnan Katsina, Farouk Lawal Joɓe ya ce gwamnati na sane da halin matsin da ma'aikata ke fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina karkashin Malam Dikko Umaru Radda ta fara ɗaukar matakan fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Gwamnatin ta kafa kwamitin mutum 15 wanda zai jagoranci tsara yadda za a fara biyan ma'aikata sabon albashi mafi ƙaranci na ƙasa.

Malam Dikko Radda.
Gwamnatin Katsina ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa sakataren gwamnatin Katsina, Abdullahi Faskari shi zai jagoranci kwamitin wanda aka ba shi mako uku ya gama aikinsa.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sa doka a Kano ana dab da fara zaɓen ƙananan hukumomi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran kwamitin zai ba da shawarwari kan yadda za a aiwatar da dokar albashi da kuma ƙarin da za a yi wa dukkan ma'aikata na kowane mataki.

Gwammatin Katsina ta san matsin da ake ciki

A wurin kaddamar da kwamitin, mataimakin gwamnan Katsina, Farouk Lawal Jobe ya ce gwamnati na sane da halin matsin tattalin arzikin ma'aikata ke fuskanta.

Farouk Jobe ya ce gwamnati ta san halin da ake ciki a ƙasar nan musamman bayan tuge tallafin man fetur.

Ya tabbatar wa mahalarta taron cewa gwamnati ta himmatu wajen tallafawa ma’aikatanta ta hanyar aiwatar da sabuwar dokar albashi ta ƙasa.

Jerin ƴan kwamitin ƙarin albashi a Katsina

Jaridar Punch ta tattaro cewa wamitin ya ƙunshi manyan jami’an gwamnatin Katsina irin su shugaban ma’aikatan gwamnati, Falalu Bawale.

Sauran sun haɗa da kwamishinonin ƙudi, kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, da harkokin kananan hukumomi da masarautu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bi sahu, ya bayyana sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata

Sai kuma mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin kwadago, wakilai daga kungiyoyin kwadago NLC da TUC da sauransu.

"Zan iya biyan N1m da noma" Gwamna Bago

A wani labarin kuma gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago ya amince zai biya mafi ƙarancin albashin N80,000 ga ma'aikata.

Gwamnan ya bayyana cewa nasarorin da jihar ta samu a ɓangaren noma, nam gaba za a iya biyan N1m a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262