Aikin Dana-Sani: Matashi Ya Shiga Hannu Bayan Yin Ajalin Danginsa Na Kusa

Aikin Dana-Sani: Matashi Ya Shiga Hannu Bayan Yin Ajalin Danginsa Na Kusa

  • Wani matashi a jihar Gombe ya shiga hannu bisa zargin ya hallaka wata mata a ranar 21 ga watan Oktoban 2024
  • Rundunar ‘yan sanda sun bayyana yadda lamarin ya faru, a halin yanzu ana ci gaba da bincike kafin gurfanar da matashin
  • Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wadannan munanan lamurran na faruwa da matasan Najeriya ba, hakan ya zama ruwan dare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Pantami, Jihar Gombe - Wani mummunan lamari ya auku a unguwar Bagadaza da ke jihar Gombe, inda wani matashi mai shekaru 31, Jonathan James ake zarginsa da kisan danginsa na kusa mai shekaru 65, Ramatu Musa.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, matashin ya kashe matar ne ta hanyar dirza mata wuka mai kaifi, har ta kai barin duniya.

An kama matashi bisa kisan mata a Gombe
Yadda aka yi ram da matashin da ya kashe mata a Gombe | Hoto: Big Daddy
Asali: UGC

‘Yan sanda sun kawo dauki

Kara karanta wannan

Sifetan dan sanda ya bindige fitaccen mawaki a Najeriya, rundunar ta dauki mataki

A cewar jami’in sintiri na ofishin ‘yan sandan Pantami, Girema Yahaya, lamarin ya auku ne da dare, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Mun samu kira mai tada hankali da misalin karfe 2:15 na safe wanda nan take muka dunguma wurin da abin ya faru. Abin takaici sukan ya kai ga mutuwar matar a sadda aka isa da ita asibitin kwararru na jihar Gombe.”

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Buhari Abdullahi ya ce, matar ta samu raunuka a kirji daga sukar wanda ya yi ajalinta da misalin karfe 1:35 na safe a ranar 21 ga watan Oktoba, Daily Post ta ruwaito.

Matakin da ake dauka a yanzu

A cewarsa:

“Wanda ake zargin, Jonathan James ya shiga hannu kuma an samu wukar da aka kisan da ita, an dauke ta a matsayin shaida.

Kara karanta wannan

Bayan kacaniyar Seamnan Abbas, sojoji sun sake tsare sojan ruwa, an gano dalili

“Rundunar ‘yan sanda na daukar wannan lamari da gaske, kuma nan kusa wanda ake zargin zai gufana a kotu.
“Mun yi Allah wadai da irin wannan aiki kuma za mu tabbatar da mai laifi ya samu hukunci daidai da abin da ya aikata a dokance.”

An kama matashi da zargin ya kashe mahaifiyarsa

A wani labarin, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mutumin mai suna Lukman Adejoju bisa zargin kashe mahaifiyarsa dattijuwa mai suna Aminat.

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu cewa Lukman, mazaunin kauyen Kajola ne da ke kusa da Apomu a jihar Osun.

Rahoton ya bayyana cewa mutumin ya kashe mahaifiyarsa, wadda aka ce tana da shekaru kusan 100 a duniya, sakamakon takaddamar da ta shiga tsakaninsu kan manja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.