Ana Fargabar Mutane 8 Sun Mutu a Hatsarin Jirgin Sama, Tinubu Ya Sa Ayi Bincike
- Ana fargabar cewa fasinjoji shida da ma'aikatan jirgi sun mutu a hatsarin jirgin da ya faru a Ribas, a cewar rundunar 'yan sanda
- Hakan na zuwa ne bayan hukumar tsaro ta tabbatar da mutuwar uku daga cikin fasinjojin, inda aka tsamo gawarwakinsu a kogi
- Bayan faruwar hatsarin, shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarni na a tsananta bincike domin gano sauran fasinjojin jirgin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ribas - Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta ce mai yiwuwa ne dukkanin fasinjoji takwas da hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu ya rutsa da su sun mutu.
Jirgi mai saukar ungulu, kirar Sikorsky SK76, mai lambar rajista: 5NBQG, mallakin kamfanin East Wind ya yi hatsari bayan tashinsa daga Fatakwal zuwa FPSO-NUIMS ANTAN.
Ana fargabar fasinjojin jirgin sun mutu
Mai magana da yawun ma’aikatar sufurin jiragen sama, Odutayo Oluseyi ya bayyana cewa fasinjoji shida ne a jirgin sai ma'aikatan jirgin biyu inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mahukunta sun ce jirgin ya yi hatsari tare da fadowa kusa da Bonny Finima a tekun Atlantika, inda aka ce ana ci gaba da aikin nemo mutane biyar bayan gano gawar uku.
A sabon rahoto, kakakin 'yan sandan Ribas, SP Grace Iringe-Koko ta yi nuni da cewa akwai yiwuwar dukkanin mutanen da ke cikin jirgin sun mutu.
Bola Tinubu ya ba da umarnin bincike
Arise News ta rahoto Bola Tinubu ya ba da umarnin a tsaurara bincike da ceto fasinjojin jirgin da ya fado a kusa da Bonny Finima a tekun Atlantika ranar Alhamis.
Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa ya ce Tinubu ya bukaci jami’an soji da ke gudanar da ayyuka daban-daban a shiyyar da su shiga aikin ceto domin ba da gudunmawa.
Shugaban ya kuma jajantawa hukumar gudanarwar kamfanin NNPCL da iyalan dukkanin wadanda aka tabbatar sun rasu a hadarin.
An gano fasinjojin jirgin East Winds
A wani labarin, mun ruwaito cewa NNPCL ya sanar da cewa jirgi mai saukar ungulu da ya yi hadari a Fatakwal a jihar Ribas na dauke da ma'aikatansa .
Wata sanarwa da NNPCL ya fitar a yammacin Alhamis, 24 ga watan Oktoba ta nuna cewa jirgin da ya yi hatsarin mallakin kamfanin East Winds ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng