Raba Kasa: Dattijon Arewa, Tanko Yakasai Ya Hango Makomar Najeriya

Raba Kasa: Dattijon Arewa, Tanko Yakasai Ya Hango Makomar Najeriya

Daya daga cikin dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya shaidawa Legit ra'ayinsa kan karuwar kiraye kiraye da wasu ke yi na a raba Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

A yan kwanakin nan, an hango daya daga jagororin a waren kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya mika wasika kasar Birtaniya ya na neman goyon baya kan samar da jamhuriyar Oduduwa.

Yakasai
Manya a Arewa sun fara fadin manufarsu kan raba Najeriya Hoto: @HonAminuSuleim/@peacock
Asali: Twitter

Legit ta tattauna da dattijo, Alhaji Tanko Yakasai da masani a fannin kimiyyar siyasa, Farfesa Kamilu Sani Fagge, sun bayyana abin da ya dace Arewa ta yi kan kokarin wasu na a rabu.

Tanko Yakasai a kan batun raba Najeriya

Kara karanta wannan

Duk da Dala ta haura N1600, IMF ya yabi kokarin CBN, ya yi ikirarin Naira ta mike

Gogaggen dan siyasa, kuma guda daga cikin wadanda su ka kafa kungiyar ACF, Tanko Yakasai ya ce masu neman a raba Najeriya ba su san abin da su ke yi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana haka ne lokacin da aka tambaye shi yadda ya ke kallon karuwar fafutukar raba Najeriya, da ma matakan da Arewa ya kamata ta dauka.

'Allah SWT ne ya hada Najeriya' - Tanko Yakasai

Alhaji Tanko Yakasai ya ce Najeriya ba za ta rabu ba saboda Allah ne Ya hada zamanta a matsayin kasa guda ba dan Adam ba.

"Duk wadannan da su ke magana a raba kasa, ba su san abin da su ke yi ba," cewar Tanko Yakasai.

Ya kara da cewa da Allah ba ya son zaman Najeriya a dunkule, da tuni yanzu Ya raba ta, kowa ya kama gabansa.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Gwamnati ta fadi yadda za a hana Dala tashi kan Naira

Yadda masana siyasa ke kallon raba Najeriya

Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Bayero ta Kano na ganin a kan yi amfani da maganar raba kasa ne saboda bukatar siyasa kawai.

Farfesan yce wannan ba shi ne karon farko da masu son cimma wata bukatar siyasa ke rajin a raba Najeriya kowa ya ja kasonsa ba.

An ba Arewa shawara kan raba kasa

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya yi zargin cewa wasu daga cikin mazauna sassan kasar nan na yi wa Arewa kallon cima zaune saboda rashin man fetur.

Fagge ya na ganin hakan ba gaskiya ba ne, duba da dimbin arzikin da ke yankin, sannan ya kuma ce shugabannin Arewa su fara shirin ko-ta-kwana na abin da zai farau a nan gaba.

Farfesa Tugga ya magantu na raba Najeriya

A baya kun ji cewa daya daga masana a Arewacin kasar nan, Farfesa Sani Lugga ya ce lokaci ya yi da mazauna shiyyar nan za su shiga hankalinsu, tare da zama a cikin shirin rabewar kasar.

Kara karanta wannan

'Sai an kula kashi': Atiku ya yi wa ministan Tinubu, Wike wankin babban bargo

Ya fadi haka ne a matsayin martani kan yadda ake samun karuwar kiraye kiraye daga Kudancin kasar nan na cewa a barke, a fitar da kasar Yarbawa da ta Ibo daga Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.