Bayan Kora, Tinubu Ya ba Ministoci Umarnin Rage Kashe Kudin Gwamnati
- Bola Tinubu ya umarci ministoci da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya su rage motocin da ke cikin ayarinsu
- Shugaban kasar ya kuma umarci ministoci da shugabannin hukumomin su rage yawan jami'an tsaronsu zuwa jami'ai biyar
- A yau Alhamis, 24 ga Oktoba ne Tinubu ya bayar da umarni domin a iya rage kashe kudin gudanarwar gwamnatinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Awanni da korar ministoci biyar tare da nada wasu, shugaba Bola Tinubu ya ba da sabon umarni na rage kashe kudi a gwamnatinsa.
Tinubu ya hana ministoci, ministocin cikin gida da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya tafiya a jerin gwanon motoci da suka wuce uku.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Olusegun Dada, mataimaki na musamman ga Tinubu kan soshiyal midiya ya fitar a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ba ministoci sabon umarni
Sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ta ce:
"Shugaba Bola Tinubu, ya iyakancewa ministoci, ministocin cikin gida da shugabannin hukumomin ghwamnatin tarayya amfani da motoci uku a ayarinsu.
"Ba za a ba su karin motoci domin zirga zirgarsu ba."
Bayo Onanuga ya ce a yau (Alhamis) ne shugaba Tinubu ya sanar da matakin rage kashe kudin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa.
An rage jami'an tsaron ministoci
Shugaba Tinubu ya kuma umurci dukkanin ministoci, ministocin cikin gida da shugabannin hukumomi da su rage jami'an tsaron da ke ba su kariya zuwa biyar.
"Tawagar tsaron za ta kunshi ‘yan sanda hudu da jami’in DSS guda daya. Ba za a ba da karin jami’an tsaro ba."
- Sanarwar shugaban kasa
Shugaba Tinubu ya umurci mai ba shi shawara kan harkokin tsaro da ya hada hannu da sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro domin sanin matakin da ya dace na rage motoci da jami’an tsaron da suke turawa.
Tinubu ya kori ministoci biyar
Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi garambawul a majalisar ministocinsa inda ya fara da sallamar ministoci biyar.
Daga cikin Ministocin da aka kora akwai ta harkokin mata da karamin Ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Gwarzo kuma Tinubu ya sanar da nada wasu sababbi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng