An Gano Ma'aikatan NNPCL a cikin Wadanda Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da Su a Ribas

An Gano Ma'aikatan NNPCL a cikin Wadanda Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da Su a Ribas

  • Kamfanin NNPCL ya sanar da cewa jirgi mai saukar ungulu da ya yi hadari a Fatakwal a jihar Ribas na dauke da ma'aikatansa
  • Wata sanarwa da NNPCL ya fitar a yammacin Alhamis ta nuna cewa jirgin da ya yi hatsarin mallakin kamfanin East Winds ne
  • NNPCL ya kuma bayyana cewa jirgin na dauke da mutane takwas kuma ya tashi ne daga Fatakwal zuwa FPSO - NUIMS ANTAN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani jirgin sama mai saukar ungulu da ya yi hatsari a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, a ranar Alhamis, na dauke da ma’aikatan NNPCL.

Kamfanin man Najeriyar ya bayyana cewa shi ne ya dauki hayar jirgin saman mallakin kamfanin East Winds domin ya yi jigilar ma'aikatansa.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan NNPCL sun mutu da jirgin sama ya yi mummunan hatsari, an rasa rayuka

Kamfanin NNPCL ya yi magana bayan jirgin sama ya yi hatsari da jami'ansa
Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa akwai jami'ansa a cikin wadanda jirgi ya yi hatsari da su.
Asali: Getty Images

NNPCL ya magantu kan hatsarin jirgi

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye wadda aka wallafa a shafin kamfanin na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da misalin karfe 11:22 na safiyar ranar 24 ga watan Oktoba 2024 ne muka samu katsewar sadarwa da jirgi mai saukar angulu, mai lambar rijista: 5NBQG
"Kamfanin NNPC ne ya yi hayar jirgin saman wanda ya tashi daga filin sansanin sojojin sama na Fatakwal zuwa FPSO - NUIMS ANTAN."

- NNPCL

'Akwai mutane 8 a cikin jirgin' - NNPCL

Akwai mutane takwas a cikin jirgin (fasinjoji shida da ma'aikatan jirgin biyu), a cewar sanarwar da kamfanin na NNPCL ya fitar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"An tuntubi hukumomin da suka dace ciki har da ma'aikatar sufurin jiragen sama, wadanda tun daga lokacin suka fitar da sanarwar manema labarai.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya su shirya: Majalisa ta ba CBN sabon umarni na janye tsofaffin Naira

A halin yanzu ana ci gaba da ayyukan nema da ceto. Ya zuwa yanzu, an gano gawarwaki mutum uku. Za mu ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki."

NNPCPL ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin tallafawa aikin nema da ceton da ake kan yi.

Jirgin sama ya yi hatsari a Fatakwal

Tun da fari, mun ruwaito cewa jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas kuma mutane uku sun mutu.

Ma'aikatar sufurin jiragen sama ce ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta bayyana cewa har yanzu ana kan neman sauran fasinjojin cikin jirgin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.