Ma'aikatan NNPCL Sun Mutu da Jirgin Sama Ya Yi Mummunan Hatsari, an Rasa Rayuka
- Jirgi mai saukar ungulu ta fadi a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers inda mutane suka rasa rayukansu
- Lamarin ya faru ne a yau Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024, jirgin saman ke dauke da mutane har takwas
- Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin sufurin jiragen sama, Odutayo Oluseyi shi ya tabbatar da haka a yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Aƙalla mutane uku ne suka rasa rayukansu bayan faduwar jirgin sama mai saukar ungulu.
Jirgin ya fadi ne a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers a yau Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024.
An rasa rayuka bayan faduwar jirgin sama
Kakakin ma'aikatar sufurin jiragen sama, Odutayo Oluseyi shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 24 ga watan Oktoban 2024, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce jirgin na dauke ne da mutane takwas ne yayin da tsautsayin ya faru a Port Harcourt, Punch ta ruwaito.
Oluseyi ya ce jirgin ya taso ne daga sansanin sojoji na Port Harcourt zuwa rijiyar mai, sai ya fada kogi.
An tsamo gawarwakin mutum 3 a Rivers
Ma'aikatar ta ce an tsamo gawarwakin mutum uku, sannan ana cigaba da aikin ceto domin nemo sauran mutanen.
"Jirgin sama mai saukar ungulu dauke da lamba, 5NBQG ya taso ne daga sansanin sojoji a Port Harcourt zuwa wata rijiyar mai."
"Jirgin mai dauke da mutane takwas ya gamu da tsautsayin ne a yankin da ya fada kogin Atlantic Ocean."
- Sanarwar
An tabbatar cewa Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo yana bakin korari domin dakile asarar rayuwa da samun raunuka.
Fasinjojin jirgi sun tsallake rijiya ta baya
Kun ji cewa an samu afkuwar masifar hadarin jirgin sama a jihar Adamawa bayan fashewar tayoyin wani jirgin saman.
Fasinjoji 199 a jirgin Max Air ne su ka tsira yayin da tayoyin jirgin guda shida su ka yi bindiga ana kokarin tashi sama.
Yanzu dai an tabbatar babu ko mutum daga da ya samu rauni, kuma tuni hukumomi su ka fara binciken fashewar tayoyin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng