Sojoji Sun Kama Wanda Ya Kafa Kungiyar Ta'addanci a Najeriya

Sojoji Sun Kama Wanda Ya Kafa Kungiyar Ta'addanci a Najeriya

  • Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan yan ta'addan IPOB da ESAN da ke ta'addanci a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
  • A yayin farmakin da sojojin suka kai, sun yi nasarar cafke wani mugu da ya jagoranci kafa kungiyar ta'addanci ta ESN a Kudu
  • Haka zalika sojojin Najeriya sun cafke waɗansu jagorin yan ta'addar kungiyar IPOB bayan kai musu farmaki a wata maboyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Imo - Rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara a Kudu maso Gabas bayan wani farmaki da ta kai.

Dakarun sojin Najeriya sun sanar da cafke wasu daga cikin manyan yan ta'addan da ake nema ido rufe.

Kara karanta wannan

Hafsan sojojin Najeriya, Lagbaja ya rasu? Rundunar ta fitar da sanarwa kan lamarin

Sojoji
Sojoji sun kama jagororin yan ta'adda. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Manjo Janar Edward Buba ne ya fitar da sanarwar nasarar da sojojin suka samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An cafke wanda ya kafa kungiyar ta'addanci

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wani mugu da ya jagoranci kafa kungiyar ta'addanci ta ESN, Pius Iguh a Kudancin kasar nan.

Daraktan yada labaran rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya ce sun kama ɗan ta'addar, Pius Iguh a yankin Orsu a jihar Imo.

An kama jagororin yan ta'adda a Abia

Haka zalika rundunar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ta cakfe wani ƙasurgumin ɗan ta'addan IPOB mai suna Emmanuel Onwugu a Abia.

Bayan zafafa sakin wuta da sojojin suka yi, sun cafke wani jagoran yan ta'adda da aka fi sani da Ifeanyi Rock da yaransa 10.

Sojoji sun harbe yan ta'adda a Kudu

Biyo bayan kama shugabannin yan ta'addar, sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe yan ta'addan IPOB har 12.

Kara karanta wannan

An barke da murna da kamfanin NNPCL da Chevron suka sake hako wata rijiyar mai

Haka zalika rundunar sojin ta yi nasarar kwato bindigogi kirar AK47 guda 10 da wasu nau'ukan makamai da tarin harsashi.

An kama yan bindiga 3 a Rivers

A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa rundunar yan sanda a jihar Rivers ta yi nasarar cafke wasu miyagu masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar yan sanda ta ce ana zargin miyagun da tare hanya da sace mutane ciki har da mai hidimar kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng