Tsohon Shugaban Hukumar NEC da Ya Shirya Zaben Abiola 93 Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Tsohon Shugaban Hukumar NEC da Ya Shirya Zaben Abiola 93 Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An shiga jimami bayan rasuwar tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Farfesa Humphrey Nwosu a Amurka
  • Farfesa Nwosu ya rasu ne bayan fama da jinya a birnin Virginia da ke kasar Amurka yana da shekaru 83 a duniya
  • Shi ya rike muƙamin shugaban hukumar daga shekarar 1989 zuwa 1993 lokacin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Humphrey Nwosu ya riga mu gidan gaskiya.

Farfesa Nwozu ya rasu ne bayan fama da jinya a birnin Virginia da ke kasar Amurka yana da shekaru 83.

Tsohon hukumar zabe a Najeriya ya rasu
Tsohon shugaban hukumar zabe ya kwanta dama. Hoto Professor Humphrey Nwosu.
Asali: Twitter

Humphrey Nwaso ya rike hukumar zaɓe

Kara karanta wannan

Jerin ministocin da Tinubu ya kora daga aiki da jihohin da suka fito a Najeriya

Leadership ta tabbatar da cewa Farfesa Nwosu ya rike muƙamin hukumar daga shekarar 1989 zuwa 1993 a mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wancan lokaci na mulkin soja,, ana kiran hukumar da NEC kafin sauya sunanta zuwa INEC bayan yi mata gyaran fuska.

Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida shi ya nada shi mukamin wanda ya jagoranci zaben 1993.

Yadda aka yi zaben 1993 karkashin Nwosu

Farfesan ya jagoranci zaben watan Yunin 1993 da mafi yawan yan Najeriya ke ganin shi ne mafi kyawun zabe a tarihin zabukan kasar da aka taba yi.

An gudanar da zaben ne tsakanin MKO Abiola a jam'iyyar SDP da Bashir Tofa da ya fito karkashin jam'iyyar NRC.

Alamu sun nuna Abiola zai yi nasara a zaben, ya zama sabon shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya aika muhimmin saƙo ga ministoci 5 da ya kora daga aiki

Daga bisani, shugaban kasa a wancan lokaci, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya umarci Nwosu ya dakatar da sanar da sakamakon zaben da aka gudanar.

Sarkin Dawakin cikin gidan Zazzau ya rasu

Kun ji cewa Sarkin Dawakin Tsakar Gida na masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Shehu Idris ya riga mu gidan gaskiya a karshen makon da ya gabata.

Alhaji Ibrahim, ɗan marigayi sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya rasu ne yana da shekaru 47 a duniya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

A wata sanarwa da masarautar Zazzau ta fitar, ta ce an yi wa marigayi sallar Jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.