'A Sayi CNG kan N200': Tinubu Ya Dauki Matakin Rage Radadin Tsadar Fetur a Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu na so a mayar da mafi yawan gidan man fetur zuwa na sayar da gas din CNG, a cewar Ekperipke Ekpo
- Mista Ekpo, wanda shi ne karamin ministan albarkatun mai (gas) ya ce kudurin Tinubu shi ne wadatar da gas din CNG
- A zantawarmu da wasu 'yan Arewa, sun jinjinawa yunkurin Tinubu kan CNG amma sun nemi a fadada shirin zuwa sauran jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana burinsa na ganin an mayar da gidajen man fetur na kasar nan zuwa na gas din CNG.
A cewar karamin ministan albarkatun mai (gas), Ekperipke Ekpo, burin Bola Tinubu shi ne wadatar da CNG da nufin rage radadin tsadar fetur.
Bola Tinubu zai sauya akalar gidajen mai
Ekperipke Ekpo, ya yi magana a kan umarnin Tinubu na mayar da gidajen man fetur na fadin kasar nan zuwa gidajen sayar da CNG inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shugaban kasa ya umarce mu da mu tabbatar da cewa an mayar da mafi yawan gidajen man fetur a fadin kasar nan zuwa gidajen sayar da CNG."
- A cewar ministan.
Ya kuma kara da cewa gwamnati za ta saukaka hanyar da ‘yan Najeriya za su bi wajen mayar da motocinsu masu amfani da fetur zuwa masu amfani da CNG.
Amfanin sayen CNG ga 'yan Najeriya
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Mista Ekpo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa a ranar Laraba.
Ministan ya bayyana kudurin Tinubu na fadada amfani da gas din CNG a Najeriya.
Gwamnati ta na ganin CNG shi ne mafi aminci, araha da kuma kare muhalli idan aka kwatanta makamashin da man fetur.
Mista Ekpo ya bayyana cewa, yayin da litar fetur za ta iya kaiwa N1,000, 'yan Najeriya na da damar sayen CNG a kan N200, wanda ke nuna samun rangwamen farashi mai yawa.
'Yan Arewa sun aika sako ga Tinubu
A zantawarmu da Nura Haruna, matashi daga jihar Katsina, ya ce shirin shugaban kasa na CNG abu ne mai kyau ga makamashi, sai dai har yanzu Arewa ba ta shaida ba.
Nura Haruna ya ce ya kamata ace zuwa yanzu an bude tashar sauya motoci daga fetur zuwa Gas a Kano, Katsina, Sokoto da Bauchi ko Gombe.
Ya ce ta haka ne kawai mutane za su iya rungumar shirin, saboda karancin gidajen man sayar da CNG na kawo nakasu ga amincewar mutane na hakura da fetur.
Janare Bature, shi ma daga jihar Katsina ya roki 'yan Najeriya da su daina sauya motocinsu zuwa CNG a wuraren da ba a amince masu ba domin gudun hatsari.
Janare ya ba da misali da abin da ya faru a wata jihar Kudu, inda mota mai CNG ta yi bindiga sakamakon an hada tankin gas din da kaya na jabu.
Domin kare faruwar hakan, Janare ya yi kira ga shugaban kasa da ya samar da wuraren sauya motocin a kowacce jiha tare da bude gidajen sayar da CNG.
Fetur ko CNG?: Tinubu ya ba da zabi
Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba 'yan Najeriya shawarar man da ya kamata su rika amfani da shi tsakanin fetur da kuma gas din CNG.
Shugaba Tinubu ya nuna cewa CNG zai wadata a kasar a kan N200 yayin da litar fetur ta kai N1000 don haka akwai bukatar 'yan kasar su rungumin tsarinsa na gas din.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng