"Ba Dole ba ne:" Najeriya Ta Soma Nuna Yiwuwar Botsarewa Shawarwarin IMF

"Ba Dole ba ne:" Najeriya Ta Soma Nuna Yiwuwar Botsarewa Shawarwarin IMF

  • Gwamnatin Najeriya ta shawarci sauran kasashe cewa ba a kowane lokaci za su yi na'am da shawarar Asusun lamuni na duniya ba
  • Ministan Kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayar da shawarar a Washington DC inda ya halarci taron IMF da bankin duniya
  • Ministan ya bayyana cewa Najeriya ta taba kin karbar shawarar IMF kuma hakan ya yi mata amfani wajen bunkasa tattalin arzikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Washington DC - Gwamnatin Najeriya ta ce ba dole sai kasashe sun rika daukar shawarwarin Asusun bayar da lamuni da sauran manyan hukumomin duniya ba.

Ministan kudi da tattalin arziki Edun ne ya bayyana haka a Washington DC da ke Amurka, inda ake gudanar da taron Bankin Duniya da Asusun Lamuni na duniya (IMF).

Kara karanta wannan

VAT: 'Yan Najeriya na fama da kansu, gwamnatin tarayya za ta sake kara haraji

tinubu
Najeriya ta bayar da shawara kan amfani da shawarwarin Asusun IMF hOTO: @Diop_IFC
Asali: Twitter

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Ministan ya ce akwai lokutan da Najeriya ta ki amfani da irin wadannan shawarwari, kuma ta ga amfanin hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta yabi shawarwarin IMF

Wale Edun ya ce duk da ba kowane lokaci ya dace kasashe su dauki shawara da IMF ta ba su ba, akwai lokutan da daukar shawarin ke da amfani.

Ya yaba da irin shawarwarin da Asusun da sauran hukumomin duniya ke ba kasashe masu tasowa wajen farfado da tattalin arzikin yankunansu.

"Taimakon IMF na da muhimmanci:" Najeriya

Kasar nan ta bayyana yadda tallafin kudi da Asusun IMF ke bayarwa ya tallafawa kasashe a lokacin cutar sarkewar numfashi ta COVID-19.

Ministan kudi da tattalin arzikin ya ce ba ya ga tallafin kudade, yadda IMF da sauran hukumomi ke bayar da shawara kan warware matsalar kudi abin a yaba ne.

Kara karanta wannan

Duk da Dala ta haura N1600, IMF ya yabi kokarin CBN, ya yi ikirarin Naira ta mike

IMF ya yabi kokarin Najeriya

A wani labarin kun ji yadda Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya yabi yadda kasar nan ke kokari wajen daidaita tare da farfado da darajar Naira da ke cikin mawuyacin hali.

Mai ba da shawara kan harkokin kudi kuma darektan harkokin kudi da manyan kasuwanni a IMF, Tobias Adrian na wannan yabo ne a daidai lokacin da ake canjin kowace Dala kan N1600.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.