Tsadar Abinci: FCCPC Ta Zurfafafa Bincike, An Gano Masu Kawo Cikas
- Hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki da abokan hulda ta kasa ta bankado mutanen da ke jawo tsadar abinci
- Mataimakin shugaban hukumar na kasa, Tunji Bello ya ce tuni wasu yan kasuwa su ka fara boye amfanin gona a bana
- Ya bayyana cewa wannan abu da su ke yi na boye kayan abinci na haddasa karancinsa, tare da jawo karin farashi a kasuwanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Hukumar da ke kare hakkin masu amfani da kayayyaki da abokan hulda ta kasa (FCCPC) ta fadi mutanen da ke da alhakin karin tsadar farashin abinci.
Mataimakin shugaban hukumar, Tunji Bello ne ya shaidawa taron yan kasuwa, masu kananan masana'antu da sauran masu da tsaki kan cinikayya hakan a Kano.
Jaridar The Cable ta tattaro Tunji Bello ya kara da cewa akwai wasu daga cikin yan kasuwa da ake zargi da aikata abin da ke sa farashin abinci ya yi tashin gwauron zabo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gano dalilin tsadar abinci
Vanguard News ta wallafa cewa hukumar FCCPC ta gano yadda wasu batagarin yan kasuwa ke haddasa tsadar farashin abinci a sassan Najeriya.
Mataimakin shugaban FCCPC, Tunji Bello ya ce yan kasuwa da ke boye kayan abinci su na taka muguwar rawa a bangaren tashin farashin a kasuwanni.
Yan kasuwa na jawo tsadar abinci
Hukumar gwamnatin tarayya ta gano cewa tuni wasu yan kasuwa su ka fara saye amfanin gona su na boye abincin a gidajen adana kayayyaki.
Hukumar da ke kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta kasa ta ce wannan na jawo rashin abinci a kasuwanni, wanda ke sanya tsadar sa a fadin Najeriya.
Yan kasuwa sun fadi dalilin tsadar abinci
A wani labarin kun ji cewa wasu daga cikin yan kasuwa a kasar nan sun dora alhakin tsadar kayan abinci da sauran kayan amfani a kan rashin tsaron da Arewacin Najeriya ke fama da shi.
Yan kasuwar sun shaidawa hukumar kare masu amfani da kayayyaki (FCCPC), bayan jami'ai sun kai samame babbar kasuwar kayan abinci ta Oseokwodo, Onitsha kan tsadar kaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng