'Aurensa Zan Yi', Matashiya Balkisu Ta Kamu Da Tsananin Son Tinubu, Ta Tura Sako

'Aurensa Zan Yi', Matashiya Balkisu Ta Kamu Da Tsananin Son Tinubu, Ta Tura Sako

  • Wata budurwa ta bayyana irin tsananin so da take yiwa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
  • Matashiyar mai suna Balkisu ta ce tana son sakon ya isa wurin shugaban kasa saboda tana son shi da aure
  • Balkisu ta ce manyan abubuwan da suka fi jan hankalinta su ne kyawunsa da kuma adalci a mulkin da yake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kano - Wata matashiya ta ba da mamaki kan soyayyar da yake yiwa shugaban kasa, Bola Tinubu a Najeriya.

Matashiyar mai suna Balkisu ta ce Allah ya jarabce ta da tsananin son Tinubu inda ta bukaci a tura masa sakon.

Matashiya ta bayyana tsananin son Tinubu da take yi
Wata matashiya, Balkisu ta nuna soyayyarta ga Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Abubakar Umar.
Asali: Facebook

Balkisu ta nuna tsananin kauna ga Tinubu

Kara karanta wannan

Awanni bayan Tinubu ya sallame ta, tsohuwar minista ta turawa shi da Remi sako

Balkisu ta fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook da Legit Hausa ta bibiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin faifan bidiyon, matashiyar ta ce tana da sakon soyayya da take son isarwa ga Shugaba Bola Tinubu.

Har ila yau, Balkisu ta fadi manyan abubuwan da suka ja hankalinta zuwa ga soyayyar Tinubu da suka hada da yadda yake gudanar da shugabancinsa da adalci da kuma kyawun da Allah ya yi masa.

Balkisu ta fadi babban burinta kan Tinubu

"Ina da sako mai nauyi da nake son isarwa ga wani babban mutum kuma mai daraja a Najeriya."
"Ina son shugaban kasa, Bola Tinubu da aure saboda yadda yake gudanar da shugabancinsa da adalci."
"Babban abin da ya fi jan hankalina shi ne kyawun da yake da shi, shiyasa nake so na aure shi."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya aika muhimmin saƙo ga ministoci 5 da ya kora daga aiki

- Malama Balkisu

Matashi ya yi wa mahaifiyar Tinubu takwara

A baya, kun ji cewa wani matashi mai suna Khamees Darazo daga jihar Bauchi ya yi bajinta bayan sauya sunan 'yarsa zuwa na mahaifiyar shugaba Bola Tinubu, Abibatu.

Khamees ya ce ya yi hakan ne ba don komai ba sai don kawai yadda ya ke tsananin son shugaban da kuma kudirorinsa kan cigaban Najeriya baki daya.

Matashin ya sauya sunan 'yar tasa mai shekaru biyu da ake kira Hauwa zuwa sunan mahaifiyar shugaba Tinubu, Abibatu saboda kaunar da yake yi masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.