Duk da Dala Ta Haura N1600, IMF Ya Yabi Kokarin CBN, Ya Yi Ikirarin Naira Ta Mike

Duk da Dala Ta Haura N1600, IMF Ya Yabi Kokarin CBN, Ya Yi Ikirarin Naira Ta Mike

  • Darajar Naira ta fara dawowa cikin hayyacinta bayan babban bankin kasar nan ya dauki kwararan matakai a ra'ayin IMF
  • Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ne ya bayyana haka a wani taro da ya gudana a Washington DC ranar Talata
  • Asusun ya jinjinawa yadda CBN ya kara kudin ruwa, ya ce yana daga daga cikin dalilan farfadowa da Naira ke yi a yanzu
  • Sai dai yanzu haka Dalar Amurka ta doshi N1700 a kasuwar canji, farashin kayan kasashen waje sun yi mugun tashi a kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Asusun lamuni na duniya (IMF) ta bayyana cewa kudin Najeriya, watau Naira na farfadowa a kasuwar canjin kudi.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Gwamnati ta fadi yadda za a hana Dala tashi kan Naira

Duk da Dala ta wuc N1600, asusun ya bayyana cewa wannan ya biyo wasu matakai da babban bankin kasar nan (CBN) ya dauka.

Tobias
IMF ya ce darajar Naira ta fara daidaita Hoto: Tobias Adrian
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa IMF ya bayyana halin da Naira ke ciki a Washington DC a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IMF: "Darajar Naira ta fara farfadowa"

Jaridar Nigerian Tribune ta tattara cewa Asusun lamuni na duniya (IMF) ya ce babban bankin kasar nan na kokari wajen daidaita darajar Naira.

Tobias Adrian, wanda shi ne mai ba da shawara kan harkokin kudi kuma darektan harkokin kudi da manyan kasuwanni a IMF ya ce ana cin nasarar farfado da kudin Najeriya.

Dalilin farfadowar darajar Naira

Tobias Adrian ya ce wasu daga dalilan da ya sa Naira ta fara dawowa hayyacinta sun hada da kara kudin ruwa da bankin CBN ya yi.

Kara karanta wannan

Yadda aka cafke Bobrisky da tsakar dare yana shirin guduwa daga Najeriya

Ya ce sauran dalilan sun hada da biyan wasu daga cikin kudin da ake bin CBN kan canjin kudi ya taimaka wajen fara daidaita darajar kudin da ke farfadiya.

Mista Adrian ya ce su na maraba da tsare-tsaren da bankin CBN ya bijiro da su kuma ya ke tafiya a kai a yanzu.

Darajar Naira ta fara farfadowa

A baya mun ruwaito cewa darajar Naira ta fara dagawa a kasuwannin bayan fage da wasu daga cikin manyan bankunan kasar nan bayan koma baya da ta ke samu.

Bayanan da aka samu daga kafar FMDQ sun nuna farashin Naira bai tashi ba duk da an samu rangwame a kasuwannin bayan fage (BDC) yayin da babban bankin kasa ya kashe makudan kudi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.