Gwamnatin Tinubu Ta Dauki Matakin karshe kan Jami'in Binance da Ta Tsare
- Bayan watanni bakwai, gwamnatin Najeriya janye dukkanin tuhume-tuhumen da take yi wa jami'in Binance, Tigran Gambaryan
- Lauyan da ke wakiltar hukumar EFCC da ta shigar da karar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a babbar kotun tarayya, Abuja
- Tun a watan Afrilu ne gwamnatin kasar nan ta tsare jami'in Binance, Tigran Gambaryan a gidan yari kan zargin safarar kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Najeriya ta janye dukkanin tuhume-tuhumen da take yi wa Tigran Gambaryan, wani babban jami'in gudanarwa a kamfanin Binance.
Watanni bakwai kenan jami'in Binance, Gambaryan ke tsare a kurkukun Kuje, Abuja kan tuhume tuhumen da suka shafi safarar kudi.
Karshen shari'ar gwamnati da jami'in Binance
A safiyar yau Laraba ne lauyan hukumar EFCC da ta shigar da karar ya sanarwa kotun cewa hukumar ta janye tuhumar da take yi wa jami'in na Binance, a cewar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake sanar da janye tuhumar, lauyan ya ce Mista Gambaryan, dan kasar Amurka, ma'aikacin Binance ne kawai, kuma an tuhume shi da ayyukan da suka shafi kamfanin.
Mark Mordi, SAN, lauyan wanda ake kara, ya amince da kudurin lauyan EFCC, yana mai cewa Mista Gambaryan ba shi da hannu a manyan hukunce-hukuncen kudi na Binance.
Amurka ta taka rawa a sakin Gambaryan
Premium Times ta rahoto cewa gwamnati ta janye tuhume tuhumen ne bayan watannin da aka kwashe ana tattaunawar sasanci tsakanin Najeriya da Amurka.
An ce wani kusoshin gwamnatin Amurka ne suka lallaba gwamnatin Najeriya ta amince da sallamar Mista Gambaryan bayan da kotu ta hana shi beli har sau biyu.
Makonni kafin hukuncin na yau Laraba, an ce wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka sun ta neman a sako Mista Gambaryan, inda suka nemi Amurka da Najeriya su sasanta.
Jami'in Binance ya fadi a kotu
A wani labarin, mun ruwaito cewa an samu wata 'yar takaddama a lokacin da Tigran Gambaryan, ya yanke jiki ya fadi a cikin wata babbar kotun Abuja.
Lauyan da ke kare jami'in na Binance, Mark Mordi, ya shaidawa kotun cewa wanda yake karewa ba shi da lafiya kuma an aika da takarda domin sanar da kotu hakan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng