"Ban Tsoron Hukumar EFCC": Gwamnan PDP Ya Fadi Dalili

"Ban Tsoron Hukumar EFCC": Gwamnan PDP Ya Fadi Dalili

  • Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ko kaɗan ba ya tsoron hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC)
  • Gwamnan ya bayyana cewa ya kamata waɗanɗa aka ba ragamar jagorancin al'umma su kasance masu gaskiya da riƙon amana
  • Ya nuna cewa zai ci gaba da ba da goyon baya ga hukumar EFCC wacce ke yaƙi da masu cin hanci da rashawa a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa ba ya tsoron hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).

A cewar Gwamna Dauda, ya kamata mutanen da aka zaɓa a kan muƙaman shugabanci su kasance masu riƙon amana da gaskiya.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya karya tarihin shekara 20, ya ƙarawa ƴan fansho alawus duk wata

Gwamna Dauda ba ya tsoron EFCC
Gwamna Dauda ya ce ba ya tsoron EFCC Hoto: Dauda Lawal, EFCC Nigeria
Asali: Facebook

Gwamna Dauda Lawal ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a wurin taro kan laifukan yanar gizo, wanda hukumar EFCC tare da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi suka gudanar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Dauda bai tsoron EFCC?

Ya bayyana cewa a matsayinsa na gwamna, ko kaɗan ba ya tsoron hukumar EFCC.

"Ba na tsoron EFCC. Me zai sa na ji tsoron EFCC? Mun zo ne don yin hidima ga al'umma, hakan shi ne mafita. Ya kamata mutane su riƙe amana. Ya kamata mutane su kasance masu gaskiya. Wannan shi ne shugabanci."

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamna Dauda zai goyi bayan EFCC

Gwamnan wanda ya bayyana cewa ba shi da masaniya kan ƙarar da wasu gwamnoni suka shigar kan EFCC, ya ce a shirye yake ya ba hukumar goyon baya.

Kara karanta wannan

Sarkin Rano ya mika bukatarsa wajen Gwamna Abba bayan an nada shi sarauta

"Wannan ne karon farko da na ji labarin ƙarar, hakan shi ne gaskiya. Don haka ban san abin da ta ƙunsa ba. Ba zan iya yin magana a kanta ba."
"Sai dai na zo nan ne domin na ba da goyon baya na ga hukumar EFCC, musamman a irin wannan lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubale kan laifukan yanar gizo."

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamna ya goyi bayan EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya yi magana kan ƙoƙarin da wasu gwamnoni ke yi na ganin an soke hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).

Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ko kaɗan bai kamata a soke hukumar EFCC ba, sai dai a ƙara ƙarfafa ta domin ta gudanar da aikinta yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng