Gwamnan Zamfara Ya Sharewa Ma'aikata Hawaye, Ya Biya Su Bashin da Suka Biyo

Gwamnan Zamfara Ya Sharewa Ma'aikata Hawaye, Ya Biya Su Bashin da Suka Biyo

  • Gwamnan jihar Zamfara ya biya ma'aikatan da suka yi ritaya kuɗaɗensu na giratuti da suka biyo bashi
  • Gwamna Dauda ya biya jimillar N9bn ga ma'aikatan da suka yi ritaya a jihar waɗanda suka biyo gwamnatocin baya bashi
  • Gwamnan ya biya N4.5bn ga ma'aikatan gwamnatin jihar da N4.9bn ga ma'aikatan ƙanananan hukumomin jihar da suka yi ritaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya biya N9bn a matsayin kuɗin giratuti da ma'aikatan Zamfara ke bin bashi tun shekarar 2011.

Gwamna Dauda ya amince da fara biyan bashin kuɗaɗen na giratuti ne a farkon watan Fabrairun 2024.

Gwamna Dauda ya biya ma'aikata hakkokinsu
Gwamna Dauda ya biya kudaden giratuti Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ya sanya a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa gwamnati ta biya N4.9bn ga ma’aikatan jihar da suka yi ritaya a rukuni tara.

Kara karanta wannan

Maulidi: Gwamnan Neja ya nuna takaici bayan jirgi ya kife da mutane sama da 300

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Zamfara ta biya ma'aikata kuɗaɗensu

Sulaiman Bala Idris ya ƙara da cewa an kuma biya ma’aikatan ƙananan hukumomi N4.5bn.

"A cikin alƙawarin da ya ɗauka na sake fasalin ma’aikatan gwamnatin jihar Zamfara, a watan Fabrairu, Gwamna Dauda Lawal ya kafa wani kwamiti da zai tantance ƴan fansho na jihar da ba a biya su kuɗin giratuti ba tun shekarar 2011."
"Ya zuwa yanzu an biya kuɗin giratuti ga mutane 2,666 daga cikin mutane 3,880 da aka tantance masu karɓar fansho, wanda ya kai N4,860,613,699.22, daga cikin kuɗaɗen da suka biyo gwamnatocin baya."
"An biya waɗannan kuɗin ne ga ma'aikatan da suka yi ritaya tsakanin shekarar 2015 zuwa 2024."
"Jimillar adadin kuɗaɗen giratuti na ma'aikatan ƙananan hukumomin sun kai N5,688,230,607.20, inda daga ciki aka biya N4,497,129,582.13. Waɗanda aka biya kuɗaɗen sune waɗanda suka yi ritaya a tsakanin shekarar 2011 da 2021.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan jinya na shirin jefa mutanen Kano cikin matsala, sun ba gwamna wa'adi

"A taƙaice gwamnatin jiha ta biya jimillar kuɗin giratuti N9,357,743,281.35 daga cikin N13,784,179,513.80 ga ma'aikatan da suka yi ritaya 6,506 daga cikin ma'aikata 8,684 da aka tantance."
"Waɗanda aka biya kuɗaɗen su ne waɗanda suka yi ritaya daga shekarar 2011 zuwa 2024."

- Sulaiman Bala Idris

Gwamna Dauda ya ba da tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ba da tallafin N100m ga gwamnatin Borno sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri.

Gwamna Lawal ya miƙa sakon jaje ne ta hannun tawagar wakilan da ya aika Maiduguri ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin Zamfara, Mallam Abubakar Nakwada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng