Najeriya Ta Yi Asarar Naira Tiriliyan 13 a Shekaru 3, Bankin Duniya Ya Yi Bayani
- Gwamnatin Najeriya ta tafka asarar N13.2tn sakamakon aiwatar da manufofinta na tallafin canjin kudin waje a shekaru uku
- Rahoton ci gaban Najeriya (NDU) da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa Najeriya ta rasa makudan kudin ne daga 2021 zuwa 2023
- A makon jiya ne ministan kudi, Wale Edun, ya sanar da cewa gwamnati ta kawo karshen tallafin fetur da na musayar kudaden waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bankin Duniya ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta yi asarar Naira tiriliyan 13.2 na tallafin kudin kasashen waje (FX) a cikin shekaru uku da suka gabata.
Manufofin gwamnati na bayar da tallafin canjin kudaden wajen sun taimaka wajen kare Naira daga daidaicewa a cikin shekarun.
Faduwar kudin Najeriya bayan janye tallafi
Gwamnatin Bola Tinubu ta dauki matakin daidaita darajar Naira ta hanyar rusa tsarin tallafin da ake badawa na canjin kudaden wajen, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma wannan matakin ne ya jawo faduwar darajar Naira, inda ake hada hadarta kan N1,600/$1 a yanzu daga N500/$1 da ake canjin kudin kafin Tinubu ya hau mulki.
A cikin rahoton da Bankin Duniya ya fitar game da asarar da Najeriya ta yi, ya lura cewa tallafin na amfanar da wasu kungiyoyi ne kawai amma kasar gaba daya na jin radadin hakan.
Gwamnatin Najeriya ta yi asarar N13trn
A rahotonta na ci gaban Najeriya (NDU), Bankin Duniya ya bayyana cewa kasar ta yi asarar Naira tiriliyan 13.2 a ga tallafin canjin kudi tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.
Punch ta rahoto cewa bankin ya ce an yi asarar Naira tiriliyan biyu a shekarar 2021, Naira tiriliyan 6.2 a shekarar 2022 da kuma Naira tiriliyan biyar a shekarar 2023.
Kafin janye tallafin canjin kudi a cikin Fabrairu 2024, biyan tallafin ya jawo asarar kudi masu yawa da kuma haddasa hauhawar kasafin kuɗi.
Gwamnati ta janye tallafin canjin kudi
Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da kawo karshen biyan tallafin man fetur da na canjin kudaden waje a hukumance.
Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya bayyana cewa wadannan tallafin sun lakume sama da Naira Tiriliyan 10 na kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng