CNG: Ana Fama da Tsadar Fetur, Tinubu Ya ba Ƴan Najeriya Zabin Sayen Lita kan N200
- Shugaba Bola Tinubu ya ce yanzu masu ababen hawa a Najeriya da zabin siyan fetur kan N1,000 ko gas din CNG kan N200
- Tinubu ya bayyana haka ne a wata ganawa da manyan jami’an kamfanin mai na NIPCO Plc a ranar Talata, 22 ga watan Oktoba
- Shugaban ya yaba da gudummawar da NIPCO ke bayarwa ga shirin shugaban kasa na tabbatar da wadatuwar CNG a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya ce ‘yan Najeriya za su iya siyan litar man fetur a kan N1,000 ko kuma gas din CNG kan N200 a kan kowane ma'aunin SCM.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da shugabannin kamfanin man NIPCO Plc a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Tinubu ya aika sako ga 'yan kasa
A cewar wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa ya fitar a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya yabawa kokarin NIPCO na samar da gas din CNG.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ce:
“Masu ababen hawa a Najeriya na iya siyan litar man fetur a kan N1,000 ko kuma iskar gas (CNG) kan kan N200 na kowane ma'aunin SCM.
“Mun kuma bullo da wani tsarin karfafawa masu ababen hawa na kasar nan ta bangaren sauya motocinsu daga man fetur zuwa iskar gas a kyauta."
Shugaban NIPCO ya yabawa Tinubu
A hannu daya kuma, Ramesh Kasangra, daraktan NIPCO, wanda ya jagoranci tawagar, ya gode wa shugaba Tinubu kan goyon bayan da yake bai wa bangaren CNG.
Kasangra ya bayyana kudurin NIPCO na karfafa hadin gwiwa da gwamnati "domin tabbatar da sauyi a makamashin Najeriya ya ci gaba da kasancewa."
Shugaban NIPCO ya tabbatar wa Tinubu cewa kamfanin na a shirye domin saka hannun jari mai yawa a bangaren samar da gidajen man CNG a fadin kasar.
NIPCO ya bude gidajen man CNG
A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin mai na NIPCO ya kammala ginawa da kuma kaddamar da sabbin gidajen sayar da gas din CNG da a Legas.
Nagendra Verma, manajan NIPCO ya bada tabbacin dorewar samar da iskar gas da kuma siyar da shi a kan N200 domin dakile radadin tsadar da fetur ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng