Ana Zarginsa da Yi wa Yarinya Ciki, Kotu Ta Ki Karbar Buƙatar Ministan Jonathan

Ana Zarginsa da Yi wa Yarinya Ciki, Kotu Ta Ki Karbar Buƙatar Ministan Jonathan

  • Tsohon Ministan Goodluck Jonathan, Kabiru Turaki ya yi rashin nasara a kotu a rigimar da yake yi da wasu mutane
  • Kotu ta ki amincewa da bukatarsa na haramta bayyana sakamakon bincike kan mahaifin wata yarinya da aka haifa
  • Mai Shari'a Aliyu Shafa ya bayyana dalilin da ya sa kotu ta yanke wannan hukunci yayin da ake cigaba da shari'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Nyanya Abuja, ta yanke hukunci kan karar da tsohon Minista, Kabiru Turaki ya yi.

Kabiru Tanimu Turaki, tsohin Ministan addini, ayyuka na musamman da harkokin gwamnati ne a mulkin Goodluck Ebele Jonathan.

Kara karanta wannan

Ministoci: Tinubu ya nada matar Ojukwu da Ministan Buhari da wasu mutane 5

Turaki
Kotu ta yi hukunci kan bukatar Ministan Jonathan Hoto: @kabiruturakisan
Asali: Instagram

Jaridar The Nation ta wallafa cewa tsohon Ministan ya nemi kotu da hana bayyana sakamakon bincike da ake yi kan waye mahaifin wata yarinya da ake tantamar ta shi ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta ki amincewa da bukatar tsohon Minista

Aliyu Shafa ya soke bukatar Kabiru Turaki na hana Uwani da wasu mutum biyu daga bayyana sakamakon tabbatar da mahaifin wata 'ya.

Wata Uwani da 'yar ta Hadiza sun zargi tsohon Ministan da mu'amala da Hadiza har ta kai ga an samu rabon diya a tsakaninsu.

Dalilin kotu na yanke hukunci kan tsohon Minista

Mai Shari'a Aliyu Shafa ya bayyana dalilin soke bukatar da Kabiru Turaki ya shigar gabanta domin akwai irin bukatar a cikin wata karar da ya shigar tun da fari.

Yanzu haka kotu ta matso da cigaba da sauraren karar zuwa 13 ga watan Nuwamba domin sauraron shari'ar bayan an tafi gwajin kwayar halitta na DNA

Kara karanta wannan

Ga mari ga tsinka jaka: Minista ya zagi mazaunan Abuja da za a ruguzawa gininsu

An tuhumi tsohon Ministan da badala

A baya mun ruwaito cewa kotu ta zauna bisa zargin da ake yi wa tsohon Minista a zamanin Goodluck Ebele Jonathan, Kabiru Turaki na yaudarar wata budurwa har ta samu juna biyu.

Ana zargin Kabiru Tanimu Turaki da yaudarar yarinya ta inda ya fara taimakonta da sama mata gurbin karatu a jami'ar Baze da ke Abuja, har ta kai ga an samu rabon 'ya a tsakani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.